Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumomi a Nijeriya sun ce an sako sauran ɗalibai 130 da aka yi garkuwa da su a jihar Neja.
Wasu ‘yan bindiga ne suka sace ɗaliban da ma’aikatan makarantar ta Katolika ta Saint Mary a a watan da ya gabata.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Sunday Dare a shafinsa na ɗ ya sanar cewa a yanzu: ‘Ba bu wani ɗalibi ko ma’aikacin makarantar da aka bari a hannun ‘yan bindga.”
Mai makarantar kuma shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Neja, Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya shaida wa BBC cewa Gwamnan jihar Neja ya tabbatar masa da alamarin.
“Gwamna ya kira ni yanzu inda ya sanar da ni cewa an sako sauran ‘yan makaranta da malamai. Ya ce na zo na karbe su,” inji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Adamu Abdullahi Elleman ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu jamian tsaro na duba lafiyar ɗaliban da malamansu kuma a ranar Litinin ne za a miƙa su ga iyayensu.”
Sai dai bai bayyana ko an biya kuɗin fansa ba.
Waɗanda aka sako na cikin ɗalibai 303 da kuma ma’aikatan makarantar ta Katolika ta St Mary 12 da ‘yan bindiga suka sace lokacin da suka kai wa ɗakunan kwana hari a ranar 21 ga watan Nuwamba.
Mahukantan makaratar sun ce wasu ɗalibai 50 sun tsere a lokacin da aka kai hari inda aka yi garkuwa da ɗalibai fiye da 200.
A farkon watan da muke ciki mahukuntan Nijeriya sun sanar da sakin dalibai 99 da kuma wani malami 1 inda aka bar akalla wasu ɗalibai 165 a hannun ‘yan bindiga.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja ya shaida wa BBC cewa mutum 130 da aka sako a ranar Lahadi kuma su ne wadanda suka rage a hannun yan bindiga inda ya ce an samu akasi kan alƙaluman farko da mahukuntan makarantar suka fitar.
ɗaliban da aka sace a jihohin Neja da Kebbi a baya-bayan nan sun sa hukumomin Nijeriya rufe makaratun sakandire na tarayya 47 kan dalilan tsaro kodayake a baya bayan nan sun sake buɗe makarantun su na masu cewa sun yi haka ne bayan da aka karfafa tsaro a ciki da kewayen makarantun
A halin da ake ciki dai, makarantu a jihar ta Neja gaba daya sun ci gaba da kasancewa a rufe yayin da hukumomin jihar suka dage cewa za su bude su ne kawai idan sun tabbatar da tsaro a cikin makarantu da kewaye.
