Cutar shanyewar ɓarin jiki gadonta ake yi — Sarkin Maganin Taraba

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Sarkin Maganin Jihar Taraba, Dakta Sahabi Abubakar, shugaban Cibiyar Sahabi Integrated Alternatiɓe Medical Centre (SIAMEC), ya bayyana cewa cutar shanyewar ɓarin jiki da aka fi sani da Stroke ba cuta ce da ke kamawa kwatsam kawai ba, face cuta ce da ake gadonta daga iyaye ko kakanni, wadda kan ɓoye a jiki tsawon shekaru kafin ta bayyana.

Dakta Sahabi, ɗan asalin Jalingo, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da ’yan jarida a makon da ya gabata, inda ya ce akasin abin da mutane da dama ke tunani, shanyewar ɓarin jiki ba ta samo asali kai tsaye daga faɗuwa ba, sai dai faɗuwar na iya kasancewa sakamakon cutar da tuni ke cikin jiki.

Ya ƙara da cewa cutar kan haɗu da wasu cututtuka kamar hawan jini, ciwon suga da cutar daji (kansa), kuma ana iya haifar jariri da ita tun daga haihuwa. Idan cutar ta yi ƙarfi, tana iya bayyana tun yaro na ƙarami, amma idan ba ta yi ƙarfi ba, kan ɓoye a jiki har mutum ya kai shekaru 40 zuwa 60 kafin ta bayyana.

A cewarsa, a mafi yawan lokuta cutar kan fara ne daga ɓangaren hagu ta gangaro zuwa dama, wanda hakan ke sa galibin masu fama da ita su faɗi ta dama. Ya ce cutar kan shafi ƙashi, haɗin gwiwa, ko jijiyoyin jiki, har ta hana mutum sarrafa hannaye ko ƙafafu yadda ya kamata.

Dakta Sahabi ya ce a cibiyarsu ta SIAMEC, suna da na’urori da dabarun da ke ba su damar gano cutar tun kafin ta yi tsanani, tare da magance ta da izinin Allah. Ya ƙara da cewa suna kwantar da marasa lafiya, kuma a wasu lokuta suna yin aikin gargajiya (tiyata ta gargajiya), musamman ga waɗanda ba su da hali, domin aikin nasu na taimako ne.

Ya jaddada cewa kafin a fara maganin shanyewar ɓarin jiki, dole ne a fara magance cututtukan da ke tattare da ita kamar hawan jini ko suga, domin samun cikakkiyar lafiya. A cewarsa, wannan hanya ta sa marasa lafiya da dama ke murmurewa cikin nasara.

Sarkin Maganin Taraba ya bayyana cewa cibiyarsu ta sha bamban da sauran wuraren maganin gargajiya, inda ya ce har fararen fata daga ƙasashen waje na zuwa domin neman magani, sakamakon irin basira da Allah Ya hore musu a wannan fanni.

A ƙarshe, Dakta Sahabi Abubakar ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ba da haɗin kai wajen kafa irin wannan cibiya a dukkan jihohi da ƙananan hukumomin Nijeriya 774, domin al’umma su amfana da wannan baiwa. Haka kuma ya yaba da kyakkyawar fahimta da ake samu tsakanin hukumomin lafiya da masu magungunan gargajiya, musamman yadda Ministan Lafiya ya halarci bikin naɗa shi Sarkin Maganin ƙasar Hausa da Sarkin Daura ya yi a kwanan nan.

By ukarofi