Makon gobe Majlisa za ta fara tantance sunayen ministocin Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dattawa ta ce ya zuwa ranar Litinin mai zuwa za ta fara tantance sunayen mutum 28 da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike mata wanda yake neman naɗa su muƙaman ministoci.

Mai magana da yawun Majalisar, Sanata Adeyemi Adaramodu (APC-Ekiti), shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Majalisar ta Dattawa.

Adaramodu ya ce duk da dai Litinin ba ranar zaman majalisar ba ce, amma la’akari da muhimmancin da ke tattare da aikin “ya sa muka dakatar da dokokinmu domin fara aikin tantancewar Litini mai zuwa.”

Ya ƙara da cewa, Majalisar za ta yi sahihiyar tantancewa domin tabbatar da an zaɓo mutane masu ƙwazon da za su taya Shugaban Ƙasa sauke nauyin da ya rataya a kansa.

“Majalisar za ta yi la’akari da ɗabi’un mutum, kimarsa, ƙwarewarsa, kuma muna da yaƙinin a ƙarshe ba za mu bai wa ‘yan Nijeriya kunya ba,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *