
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT) ta umarci dukkan malaman makarantun sakandare a Jihar Oyo da su janye daga ayyuka daga yau Litinin, 1 ga watan Yuni, 2026 har zuwa lokacin da za ta yi kira.
A cewar umarnin, wanda jagorancinta na ƙasa ya fitar, an shirya yajin aikin ne don nuna adawa da cigaba da garkuwa da malamai da ɗalibai, waɗanda har yanzu batun ceto su yana halin rashin tabbas.
Ya ce, cigaba da jinkirin ceto mutanen ya haddasa tsoro da ɗimuwa acikin malamai da karya gwiwar iyaye wajen tura ‘ya’yansu makaranta a ƙauyukan sassan jihar.
Hakan na zuwa ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya a ranar Lahadi ya umarci a ɗibi jami’an kula da ƙauyuka (forest guards) guda 1,000 domin ceto malamai da ɗaliban.
A sanarwar, wadda ke ɗauke da sanya hannun Shugaban NUT na Oyo, Kwamared Hassan Fatai, ya ce sun ɗauki matakin zanga-zangar ne domin janye hankalin hukumomin gwamnati akan buƙatar gaggawa ta ceto mutanen ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, ƙungiyar ta roƙi malamai da su tabbatar da bayar da ciki haɗin kai ga da kuma zama a gidajensu har na tsawon lokacin.
