
Daga BELLO A. BABAJI
Kocin ƙungiyar Manchester City, Pep Guardiola ya ce ƙungiyar ta shiga halin rasa damar samun gurbi shiga gasar cin kofin zakarun Nahiyar Turai, wato UEFA champions league.
Ƙungiyar ta jera shekaru 14 tana haskawa a gasar inda har ta gai ga nasarar lashe kofin a 2023.
A halin yanzu Manchester City ke mataki na bakwai bayan wasanni 17 a gasar Premier league.
Sannan, ƙungiyoyin ƙasar Ingila sun samun gurbin ƙarin ƙungiya ɗaya a Champion league saboda bajinta da suke nunawa a gasar.
