
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Ahmad, ya yi kira ga hukumomi da su yi bincike game da kashe wasu fararen hula goma da wani jirgin sojojin sama mai tashin angulu ya yi a yayin yaƙar ta’addanci a ƙauyukan Gidan Bisa da Runtuwa a jihar.
Gwamnan ya yi addu’ar fatan samun rahamar Allah da kuma haƙurin juriya ga ƴaƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a lamarin wanda ya auku a ranar Laraba.
Ya kuma bada tallafin Naira miliyan 20 da buhunan kayan abinci ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa ta hannun Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muhammad Bello Sifawa.
A cikin wani saƙon da Sakataren yaɗa Labaran Gwamnan, Kwamared Abubakar Bawa ya fitar, ya ce ciyaman ɗin ƙaramar hukumar Silame da abin ya faru, Abubakar Gitta Rana ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na safe a lokacin da wasu jiragen yaƙi biyu suka sako boma-bomai da ya yi sanadiyyar kashe mutanen da ma wasu dabbobi.
Sanarwar ta kuma ce gwamnan tare da Sanata Aliyu Maga-Takarda, wato jagoran jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar da kuma Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Muhammadu Maigari Dingyaɗi sun yi addu’ar samun rahamar Allah tare da aika saƙon ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan.
