Manyan abin kunyar iyali shida da suka girgiza 2021 a Nijeriya

Wasu fitattun iyalai a Nijeriya sun tsunduma cikin cece-kuce da ya sa aka shiga kace-nace a Nijeriya kan halin da su ke ciki a wani lokaci a bara, 2021. Kafofin yaɗa labarai, musamman kafafen sada zumunta sun yi ta magana kan rigingimun. Wasu daga cikinsu batun na su bai daɗe ba aka watsar, inda wasu kuwa har yanzu ana ɗaga batun.

Tsohon Sufeto Janar Idris Kpotun da amaryarsa Asta:
Tsohon Sufeto Janar na ’yan sandan Nijeriya, Ibrahim Idris Kpotun ya shiga cikin rikicin aure da matarsa ne tun a shekarar 2017, lokacin da ya auri Amina Asta, mataimakiyar Sufurtandan ’yan sanda (DSP) haifaffiyar jihar Kaduna. Hakan ya sa tsohon Sufeto Janar ɗin ya raba gari da matarsa ta farko Barista Asmau Ndayako, ’yar gidan sarautar Nupe a shekarar 2018. Daga nan har zuwa ƙarshen shekarar da ta gabata, labarin ya kasance wani lamari na daban kamar yadda aka ruwaito cewa hakan ya sanya shi nesantar ‘ya’yansa na haihuwa; An tilasta wa Kpotun sanya hannu kan takardar saki na matarsa ta farko, sannin kuma cewa tsohon Sufeto Janar ɗin na cikin ruɗani kuma ‘yan uwansa sun yi ƙoƙarin kuɓutar da shi, yayin da kuma aka ji cewa sabuwar matar ta yi ƙoƙarin sauya sunayen mafi yawan kadarorin da ya mallaka tsawon shekaru zuwa sunanta. Sauran abubuwan da suka biyo baya sun haɗa da rabuwar Asta a mataki na uku da Kpotun ya yi bayan shiga tsakani da danginsa suka yi, waɗanda suka yi imanin cewa ɗan uwan nasu ya kasance cikin asiri ne da sabuwar matar ta yi masa, wannan ya biyo bayan dawowar ma’auratan daga aikin hajji. Rahotanni sun ce Asta ta ci gaba da zama a otal ita kaɗai inda ta ke barin Kpotun yana gudanar da aikin Umrah shi kaɗai. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naza Kpotun ne a ranar 21 ga Maris, 2016, kuma ya riƙe muƙamin IGP har ya yi ritaya a watan Janairun 2019.

Fani Kayode da matarsa Chikwendu:
Ga tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, taƙaddamar aurensa ta taɓarɓare tun shekaru da suka gabata tare da matarsa Precious Chikwendu. Abubuwa sun ta faru tsakaninsu na tuhume-tuhume da zarge-zarge da kuma zargin cin zarafi da nuna rashin imani yayin da suke tare. A ranar 6 ga Maris, 2021, Fani-Kayode ya sami hujjar mayar da martani ga ikirarin da Chikwendu ta yi a wata kotu inda ta ba da shaidar cewa Fani-Kayoda yana cin zarafinta. Neman wajen wanda wanda ‘ya’yansu maza huɗu za su zauna a wajensa ne babban dalilin da ya haifar da rikicin. Chikwendu wadda ta zarge shi da cin zarafi da dama ciki har da lokacin da ta ke ɗauke da juna biyu, tana neman a ba ta cikakken ɗaukar ɗawainiyar ‘ya’yansu maza huɗu, ta yi wannan zargin ne a wata takardar rantsuwa da ta rubuta don nuna goyon wani ƙudurin da aka kawo bisa sashe na 69 na dokar kare haƙƙin yara, 2003. Chikwendu, wacce ta yi zargin cewa tsohon ministan yana hana ta haɗuwa da ‘ya’yanta na tsawon watanni, ta roƙi kotu da ta tilasta Fani-Kayode ya riqa biyanta Naira miliyan 3.5 duk wata domin kula da yaran huɗu. An fitar da labarin rabuwarsu ga jama’a a watan Satumbar 2020.

Sarki Ooni na Ife da amaryarsa Annabiya Naomi:
Ga dukkan alamu dai abubuwa suna tafiya daidai ga Ooni na Ife Oba Adeyeye Ogunwusi a cikin shekaru uku da aure tare da ɗaya daga cikin matansa Annabiya Naomi Silekunola, kwatsam sai labari ya yi kaca-kaca da taƙaddamar rabuwa tsakanin ma’auratan. An zargi mahaifiyar Naomi da hannu a matsayin dalilin matsalolin aure. Nuna rashin ɗa’a da ziginta suka yi sanadiyyar mutuwar auren ’yarta. Al’amura sun yi kunnen uwar shegu makonni uku da suka wuce lokacin da Olori Naomi ta fito fili ta kashe aurenta da sarkin tana mai cewa ba za ta iya jurewa ɗabi’un sarkin ba.

Ohakim da Amuchienwa:
Ranar 28 ga Oktoba, 2021 ce ranar da za a fara shari’ar Chinyere Amuchienwa Igwegbe da ’yan sanda ke tuhumarta da laifin bayar da bayanan ƙarya a wata takarda da ta rubuta a kan tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim. Sai dai, ba a tabbatar da ko an fara shari’ar ba a lokacin da aka rubuta wannan rahoto. Wannan shari’ar na kotu wani ɓangare ne na ƙarar da Ohakim ya shigar na zargin cin zarafi, barazana ga rayuwa da kuma karvar kuɗin fansa a kan Igwegbe ɗan asalin Imo mazaunin Legas. Mai shari’a Halilu Yusuf na babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli, 2021 ya bayar da belin Igwegbe, uwargidan Ohakim.

Ɗan Ganduje da mahaifiyarsa:
Ita ma kujerar gwamnatin jihar Kano ta samu matsala a cikin shekarar da ta gabata a lokacin da ɗan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Abdulazeez a ranar 13 ga watan Satumba ya kai ƙarar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC. Abdulazeez ya zargi mahaifiyarsa da laifin cin hanci da rashawa da kuma zamba a fili, saboda haka hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta miƙa goron gayyata ga uwargidan gwamnan jihar Kano da ta bayyana a gabanta a ranar 9 ga watan Satumba a hedikwatar Abuja domin amsa waɗannan tuhume-tuhumen. Uwargidan Ganduje ta yi watsi da gayyatar EFCC kuma a ranar 14 ga Satumba, ta tashi zuwa Landan don halartar taron kammala makarantar ɗaya daga cikin ’ya’yanta. Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulazeez ya gudu zuwa Dubai bayan faruwar wannan lamari mai cike da cece-ku-ce.

Ɗan Gwamna Kure da mahaifiyarsa:
Jihar Neja ta farka ne a ranar ƙarshe ta watan Janairun 2021, inda aka samu labarin cewa, ɗaya daga cikin ’ya’yan marigayi tsohon Gwamna Abdulkadir Kure, Umar Abdulkadir Kure, ya kai ƙarar mahaifiyarsa, Sanata Zainab Kure zuwa kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a na jihar Neja yana ƙalubalantar rabon gadon mahaifinsa da wata Kotun Shari’a ta raba. Umar wanda ya haɗa da sauran ‘yan uwansa Ibrahim Abdulkadir Kure, Khalifa Abdulkadir Kure, Nureini Abdulkadir Kure da Khadijat Abdukadir Kure, ya roƙi kotun da ta ƙara masa damar neman izinin ɗaukaka ƙara, da kuma ƙarin umarnin kotun ɗaukaka ƙara ta Shari’a ta ɗaukaka ƙara da kuma umarnin ƙara tsawaita wa’adin na lokacin da za a shigar da sanarwar ɗaukaka ƙara a kan cewa kotun ƙolin ba ta yanke hukuncin ba har sai da kwanaki 30 da za a ɗaukaka ƙara. Umar ya ce, a cikin takardar rantsuwar cewa bai gamsu da kotun da ke shari’ar kula da rabon gadon mahaifinsu da ya rasu ba. Umar Abdulkadir ya kuma ƙalubalanci rabon kadarorin mahaifinsa ba tare da biyan duk wani bashin da aka binne marigayin da su ba, kuma ba a yi masa adalci ba wajen rabon kadarorin. Ba a sake jin wani abu ba bayan wannan shari’ar na kotu kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *