Marigayi Lawal Sa’idu Funtua shahararren marubuci ne, inji Dujiman Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai kuma Dujiman Katsina, Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed ya nuna alhininsa kan rasuwar ɗaya daga cikin sanannun ƴan jarida a Najeriya, Sa’idu Funtua.

Marigayin ya rasu ne ranar Alhamis da ta gabata bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya.

A wata takarda da jami’in yaɗa labarai, Sardaunan Francis ya fitar, ɗan majalisar ya bayyana Lawal Sa’idu a matsayin ƙwararren dan jarida da al’umma ke alfahari da shi kan faɗin gaskiya komai ɗacinta .

Ya ce rayuwarsa a aikin jarida yafi mayar da hankali wajan rubuce-rubuce kan matsaloli da suka shafi alummomi da abinda ya shafi harkokin siyasa da gwamnati za ta daɗe tana tunawa da shi.

Dujiman Katsina ya ƙara da cewa marigayi Sa’idu Funtua lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban ƴan jarida reshen kafofin yaɗa labarai a Katsina ya nuna ƙwarewa da kamanta gaskiya da adalci wajan shugabancin kungiyar.

Hon. Aliyu Ahmed wanda ke wakiltar mazaɓar Musawa da Matazu ya jawo hankalin al’ummar jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya da su yi amfani da darasin da suka koyan kan rubuce-rubuce da halayensa da ya nuna a lokacin da ya ke raye domin bada tasu gudunmawa wajen raya aikin jarida.

Dujiman ya kuma yi ta’aziyya ga ƴaƴan ƙungiyar kan babban rashi da suka yi inda ya ce babu shakka marigayi Lawal Sa’idu Funtua ya bar wani giɓi da zai wuyan cikawa a akin jarida a jihar Katsina da ƙasa baki daya.

Marigayi Lawal Sa’idu Funtua ya rasu yana da shekara 58 inda ya bar mata biyu da ya’ya tara.