Martani: Muƙabalar Kano

Daga ALIYU SAMBA

Naso a ce yadda ka faɗa a farko ɗin ka aikata, shi ne baka so ka ce komai ba dan cewar ka ba za ta hana ba, a lokaci guda kuma ba za ta sa ba, to amma sai ya zam cewa malam ya magantu ta irin usulubin da nake ganin ya kamata ace ya sake bitar abubuwan nan yadda ya kamata.

A zaton da nake wa Malam Saleh Ƙaura shi ne, mutum ne da zai ƙoƙarin yin adalci ga kowa ba tare da la’akari da saɓanin dake tsakanin su ba, sashen rubuce rubucen sa suna cike ne da bayanai da kuma jan hankali wanda a aikace anan kaman ya samu tuntuɓen tabbata akan su.

Da farko tunda malam ka soma da batu akan addu’a da kace kun duƙufa kuna yi na hana Sheikh Dr Abduljabbar Kabara duk wata dama da karatun sa (wanda ka kira baƙar guba) zai isa zuwa kunnen muminai ko da wanne irin suna ne, sai nake son na fara da tambayoyi kamar haka, Akaramukallah;

  1. Shin kore hadisan da suka nasbatwa Annabi SAW jima’i da mata 11 a lokaci guda ne baqar guba ko kuma tabbatar dashi?
  2. Shin ƙoƙarin nisanta Annabi da dukkan nau’in assha shi ne baƙar guba ko kuma tabbatar masa?
  3. Shin kira zuwa ƙanƙamewa ahlul baiti a bayan Alƙur’ani shi ne baƙar guba ko kuma kira zuwa akasin sa?
  4. Shin fifita ahlul kisa’i akan dukkan al’ummar Annabi SAW shine baqar guba ko kuma fifita wasu a a kan su?

Ina jin  akwai bukatar malam ya amsa mana waɗannan dan mu tabbatar da cewa abinda ya kira baƙar guba ya tabbata a gubar, ko kuma kawai an nasabta mana ne saboda savani da ake dashi da tafiyar ko kuma dan rusa ƙimar tafiyar ashabul kahfi.

A zato na a musulunci da kuma kundin tsarin mulki ƙasa, baka taɓa yi wa mutum hukunci akan aikata laifi ba tare da ka yi magana da shi ba, ka kuma ji daga gare shi ba. A lokacin da aka samu wasu marasa tsoron Allah sun daddatso wurare da ake yayatawa suna nasabta ma Sheikh Dr Abduljabbar Kabara taɓa alfarmar Annabi, abinda yake wajibi ga mahukunta shi ne kiran sa, da bijirar masa da waɗannan abubuwan dan a tabbatar da gaskiyar al’amarin, akaramukallah me yasa kuke gaba da wannan adalcin na fito da gaskiya dan tabbatar da adalci.

Anya kuwa ba wani lauje a cikin naɗi kuwa, duba da cewa an samu waɗanda kun tabbatar da cewa suka suke ga janabin Annabi daga cikin ku, har yanzu suna da rayuwa tare da ku, kuma muna ganin su suna gudanar da al’amuran  su a Facebook, muna jin su a wajen taru kan maulidi?

Meyasa ba za a tattauna da shi ba bayan Allah yayi umarni ga Musa da ya je wa fir’auna da ya ce shi Allah ne, ya tattauna dashi cikin girmamawa da lafazi mai taushi, shin zunubin da ake tuhumar malam Abduljabbar dashi in ya ma aikata din yakai munin mutum yace shi ne ubangiji? Me yasa baza a zauna dashi ba a ji daga gareshi kafin hukunci tunda an samu bayani daga gare shi cewa sharri akai masa?

Me yasa ma za a ƙi zama dashi muddin abinda ake tuhumar sa da shi gaskiya ne? Ya kamata duk mai tunani yayi wa kan sa wannan tambaya, idan Allah zai ce da masu nasabta masa ɗa su kawo dalilin su, me ya sa ba za a ji daga malamin ba, ko dai kawai ƙirƙira masa akai tunda an rasa makamin kaishi ƙasa?

Wacce hujja ce za a baiwa al’umma bayan wacca aka basu, ko akaramukallah ayi yanda kuke so shi ne adalci, a faranta muku takan tauye masa haƙƙi da kuma haramta masa damar da yake da ita na ɗan ƙasa?
Babban hatsari a cikin al’umma rashin gaskiya da rashin adalci wanda shi ne tushen dake assasa fitina.

Kuma babu musulmin kirki da zai murna da haka hatta akan kafiri, balle ɗan’uwan sa musulmi. Idan gwamnati ta so amfani da umarnin da Allah yayi wa muminai cewa “In an zo muku da labari ku niƙadin sa, kada kuyi hukunci da labarin ɓangare guda ku wayi gari cikin nadamar hukuncin ku.”

Ban tsammaci mumini zai gaba da yunƙurin maslaha a umarnin nan ba, saidai nafi kallon cewa watakil bashariyya ce ta ɗan motsa wa Malam Saleh yake ganin goyon bayan abinda ya yi hannun riga da adalci zai taimaka masa wajen rigima da abokin savanin sa. Hakan kuma na ga ya ci karo da kiran da yake yi tsawon shekaru kan kyautatawa abokin savani da yi masa adalci.

Allah ya ganar damu ya gafarta mana, Allah ya sa mu zama masu adalci hatta akan maƙiyan mu.