Muƙabalar Kano

Daga SALEH ƘAURA

Ban so na ce komai ba, saboda na san magana ta ba za ta sa ba, ba kuma za ta hana ba, amma dai ganin cewa da alama addu’ar da muka duƙufa muna yi na Allah ya hana duk wata dama da za a yaɗa wannan baƙar guba ta isa zuwa ga kunnuwan muminai koda da wani irin suna ne, ta amsu, shi ya sanya na ce bari in gabatar da waɗannan tambayoyi, domin dai tsakani da Allah abin mamaki yake ba ni, ya kuma yi matuqar ɗaure mini kai:

1) An ce gwamnatin Kano, ta rufe Masallaci da makarantar Abdujjabbar Kabara da makarantarsa, ta kuma haramta sanya karatuttukansa a kafafen yaɗa labarai da sadarwa, mene ne dalilin gwamnati na ɗaukar wannan mataki?

Babu shakka ya kamata a ce an ɗauki wannan mataki ne bayan bincike da samun hujjoji da dalilai, abin tambaya a nan shi ne: mene ne kuma ya sanya ita gwamnatin ta juyo da baya da wani salo da zai bai wa wannan mutumi matsayin da ba shi damar a saurari miyagun abubuwan da yake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai kai – tsaye (live), ba kuma tare da cewa gwamnatin ta sake samun wasu hujjoji ko dalillai da za su sanya ta ajiye matakin da ta dauka jiya ba, bayan da ma wannan ne dalilin da ya sanya gwamnati ta haramta masa yin karatu, kai har ta kai ga yi masa ɗaurin talala?!

A zato na malamin da kansa in ba ta wannan damar da gwamnati take neman ta ba shi ba, ba zai iya isar da abin da yake dakonsa zuwa ko’ina a faɗin ƙasar nan kaman yanda wannan lashe amai da gwamnatin yake neman ya ba shi ba.

2) Gwamnati ta bakin Gwamna ta ce, an daɗe ana ankarar da ita akan abubuwan da wannan mutumi yake yi, amma ba ta ɗauki mataki ba sai da ta jira aka kawo mata hujjoji da dalilai, kuma su ƙin aka kawo mata ta ɗauki matakin rufe Masallaci da makarantarsa, da ma yi masa ɗaurin talala.

Saboda haka, idan dai har gwamnati ta yarda yanzu da a zo a yi zaman muqabala da shi. To al’umma za su so su ji irin hujjoji da dalilai da kuma tsawon lokacin da aka ɗauka ana isar mata da waɗannan hujjoji da dalilai da ta aminta da su. Na dai san bai kamata hujjoji da dalilan su tsaya a barazanar kayar da gwamnati a zaɓe mai zuwa, ko kalaman magiya da tumasanci da yin amai da lashewa da malamin ya yi ba.

Ya kamata dai gwamnati ta yi aiki da abin da yake a gabanta, wanda hujjoji da dalilansa suka zo mata, bayan bincike da bin ƙwaƙƙwafi kaman yanda ta bayyana a baya, in kuma abin da ta faɗa ba haka ba ne, sai ta fito da faɗa wa al’umma.

Saboda waɗannan abubuwa, da ma wasu da suka fi su hatsari ne ba na goyon bayan yin muƙabala da Abdujjabbar Kabara, domin zaman zai zamo wasila ce ta yaɗa ɓarna, bugu da ƙari kuma ni tun tuni na gama gamsuwa da cewa matsalar Abdujjabbar Kabara ba ta jahilci ne da za iya warware ta da ilimi ba, ba saɓani ne na malamai da za a warware bayan zama akan teburi ba, matsala ce da ke cike da son zuciya, ita kuwa son zuciya ba shi da magani sai Allah, (Shin ba ka ga wanda ya ɗauki son zuciyarsa ya riƙe ƙyam tamkar yanda muminai suke riƙo da Ubangiji ba ne, wanda Allah ya ɓatar da shi duk da ilimin nasa, ya kuma rufe jinsa da zuciyar sa, ya kuma kawo yana ya rufe idanuwansa da ita, wane ne zai iya shiryatar da shi in ba Allah ba, ashe bai kamata ku yi tunani ku gane haka ba?!) [al- Jasiya: 23].

Allah mun tuba Ka yafe mu, kada Ka kama mu da son zuciyar da wasu suke tafkawa da sani, ko da jahilci, amin Ya Rabbal alamin.