Gwamnati ta ƙaddamar da rukunin ‘C’ na shirin N-Power

  • An fitar da matakan da masu shiga shirin za su bi

Daga WAKILIN MU

Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen dogon jiran da ake yi na fara aiwatar da rukuni na uku (Batch C) na shirin N-Power wanda za a shigar cikin jerin shirye-shiryen rage matsin rayuwa, wato National Social Investment Programmes (NSIPs).

Mai bada shawara kan aikin jarida ga Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Madam Nneka Ikem, ita ce ta bayyana haka a ranar Alhamis cikin wani saƙo da ta tura a Twitter.

A cewar ta, ana kira ga dukkan waɗanda su ka cike takardun nema shiga shirin da su ci gaba da sauraren bayanai kan tantancewar su.

Ta rubuta cewa: “Labari da ɗumi-ɗumi! Za a ƙaddamar da @npower_ng rukuni na C a yau a manhajar @NSIP_NG wato NASIMS.

“Masu neman shiga #BatchC su ci gaba da duban fitowar bayanai kan tantancewar su. @nairaland @NigerianYouthC2 @Npower_Reps”.

Idan an tuna, kimanin matasan Nijeriya miliyan biyar ne su ka rubuta takardar neman shiga shirin N-Power a cikin 2020. Rajistar shiga kashin farko na shirin an fara ta ne a ranar 26 ga Yuni, 2020, kuma manufar shirin shi ne a sama wa matasa 500,000 aikin yi.

A cewar minista Sadiya Umar Farouq, ana so ne a sama wa matasa damarmaki da za su ƙware ta yadda za a iya ɗaukar su aiki ta hanyar ba su dabarun yin sana’a.

Tun ba a je da nisa ba, a yau ne ma’aikatar ta bada sanarwar cewa duk wanda ya cike buƙatar shirin na N-Power ya shiga mataki na gaba na rukunin ‘C’ kamar yadda aka ce za a sanar.

Saboda haka a sanarwar da Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura Alkali, ya bayar a yau, ma’aikatar ta yi
kira ga dukkan waɗanda su ka nemi shiga cikin rukunin da su gaggauta bin waɗannan matakan ba tare da ɓata lokaci ba:

  1. Su duba imel ɗin su da su ka bayar lokacin neman shiga shirin domin ganin matakan da za su bi su shiga gidan yanar shirin.
  2. Su shiga www.nasims.gov.ng domin shiga gidan yanar masu neman a ɗauke su a shirin saboda su bada ƙarin bayanan da ake nema game da su.
  3. Su bi umarnin da aka jera a gidan yanar tare da yin jarabawar intanet da aka tsara a wajen.