Masanin Zambiya: Takunkumin ƙasashen Yamma na haifar da illa ga tattalin arzikin duniya

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kwanan nan ne a yayin da yake zantawa da kafar CMG, shahararren masanin siyasa na ƙasar Zambiya, Neo Simutanyi ya ce, Rasha, babbar ƙasa ce dake fitar da alkama da makamashi, kuma irin takunkuman da Amurka da sauran wasu ƙasashen yammacin duniya suka sanya mata, sun riga sun haifar da mummunar illa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar duk duniya.

Mista Simutanyi ya bayyana cewa, duba da takunkuman da aka ƙaƙƙaba mata, Rasha ta ƙasa halartar harkokin kasuwancin ƙasa da ƙasa, kana, ba za ta iya fitar da wasu manyan hajojinta zuwa kasuwannin duniya ba. Rikicin Rasha da Ukraine ya kawo mummunar illa ga tattalin arzikin duniya.

Fassarawa: Murtala Zhang

By Editor