Da Ɗumi- ɗumi: Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha ƙawayan

Daga BASHIR ISAH

Bayanan da Manhaja ta kalato na nuni da cewa, jami’an hukumar EFCC sun yi wa gidan tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Okorocha da ke Abuja ƙawanya.

Naija News ta ruwaito cewa, baya ga jami’an EFCC haka nan, an ga ‘yan sanda a wajen ɗauke da bindigogi.

Majiya da ga EFCC ta ce kafin wannan lokaci, hukumar ta gayyaci Okorocha sau da dama domin ya amsa mata tambayoyi masu alaka da zargin almundahana amma ya ƙi amsawa.

Ya zuwa haɗa wannan labari ba a ji komai ba daga bakin kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, kan batun.

Idan dai za a iya tunawa, a Janairun da ya gabata EFCC ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Abuja a kan Sanata Okorocha da wasu bisa zargin haɗin baki wajen wawushi biliyan N2.9 mallakar gwamnati.

EFCC ta kai Okorocha kotun ne a daidai lokacin da ya bayyana ra’ayinsa na shiga takarar Shugaban Ƙasa.