Wani masallaci ya bayyana shekara 37 bayan nitsewarsa cikin wata madatsar ruwa da ke ƙasar Indiya
Masallacin, wanda ake yi masa laƙabi da Masjid Noori ya nitse ne a madatsar ruwar Phulwaria da ke jihar Bihar a shekarar 1985 yanzu kuma da ruwan ya janye sai ya ga shi ya bayyana bai rushe ba.
Mutanen yankin sun ce masallacin ya daɗe a wurin kafin a soma ginin madatsar ruwar, wanda hakan ta sa aka kwashe mutanen yankin tare da matsar da su zuwa wani wuri a 1979.
Bayan tashin jama’a an bar masallacin a yashe, a inda bayan gama aikin madatsar ruwar, ruwa ya mamaye yankin baki ɗaya har ya shanye kan masallacin a inda nutse ba a ganin ko alamarsa, ƙarancin ruwa da kuma fari da ake fama da shi a yankin a yanzu haka, ta sa madatsar ruwan ta kafe.
Wannan ya sa masallacin ya bayyana, kuma a tsaye kamar yadda ya ke a da, bai kuma rushe ba.
Bayyanar masallacin ta sa mutane na ta tururuwa cikin taɓo da laka zuwa ganinsa suna kuma shiga cikinsa.
An kiyasta shekarun ginin masallacin 120 a duniya, la’akari da tsari da kuma yanayin gininsa, a cewar masana.
