Ma’aikaciyar banki mai juna biyu ta haihu a gidan yari

Spread the love

Hankalin jama’a ya tashi a Jihar Osun biyo bayan tsare Awanat Ajayi, wata ma’aikaciyar banki mai ɗauke da juna biyu da ta daɗe a gidan yari na Ilesa.

A baya kakakin rundunar ’yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya sanar da kama manajan bankin First Bank, Talabi Adeniyi, bisa zargin almundahanar Naira miliyan 650 na hada-hadar kuɗi ta POF. Ajayi, ɗaya daga cikin ma’aikatan banki da ke aiki a ƙarƙashin Adeniyi, an kama ta ne bayan da aka ce ta bai wa Alƙalin Kotun Mai shari’a Oyindamola Daramola kuɗi a wani ɓangare na cin hanci da rashawa.

Rikicin ya samo asali ne daga zargin Talabi na asarar Naira miliyan 650 a harkar kasuwanci.

Daga bisani an gurfanar da Ajayi a gaban wata kotun majistare ta jihar Osun, ƙarƙashin jagorancin alkalin kotun, Olusegun Ayilara, kan karɓar naira miliyan 10 daga hannun Daramola. Duk da roƙon da lauyanta ya yi na neman beli, yana mai nuna cewa tana da ciki da kuma gano cutar Hepatitis, kotu ta tasa ƙeyar ta zuwa gidan yari.

A watan Agusta, Alƙalin Kotun Mai shari’a Ayilara, ya bayar da belin ta bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri, inda ya buƙaci sarki ko jami’i mai matsayi na 14 da ya tsaya mata, tare da ba da kuɗi Naira miliyan 5 domin a sake ta.

A yayin zaman kotu a ranar Laraba, lauyan Ajayi ya sanar da kotun cewa ta haihu ne ta hanyar Cesarean a lokacin da take tsare. Sai dai alƙalin kotun mai shari’a Ayilara ya jaddada cewa uzuri haihuwa ba ya a matsayin dalilin tsagaita shari’a, yana mai cewa, “Sharaɗin belin matar bai cika ba, kuma bayar da beli ba sake ba ne. Wannan ita ce doka, kuma ko da ni ba ni da ikon soke ta; babbar kotu ce kawai za ta yanke hukunci.”

Lamarin dai na ci gaba da tayar da hankalin jama’a, inda da dama ke nuna shakku kan yadda ake yi wa mata masu juna biyu a fannin shari’a, musamman a irin wannan mawuyacin hali.

By ukarofi