Ko kun tuna jirgin Titanic?

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

A shekarar 1912 jirgin dakon fasinja mafi girma da kayan alatu a tarihi zuwa wannan lokaci ya tashi daga gaɓar ruwan Southampton da ke ƙasar Ingila a tafiyarsa ta farko zuwa birnin New York da ke Amurka.

Matuƙin jirgin, Edward John Smith, saboda ganin yadda aka gina jirgin, har kuri ya yi cewa, “ko Allah ba zai iya nutsar da jirgin ba”. To, wannan jirgi dai bai isa Amurka ba, saboda a hanya ya yi karo da wata ƙanƙara (iceberg), wadda ta yi sanadiyar nutsewarsa ranar 15 ga April, 1912.

Amma bayan karon, kafin jirgin ya nutse ya ɗauki kusan awanni uku ya na nutsewa. A lokacin da ya yi karon, wani sashe na ƙarƙashin jirgin ya fashe, ruwa ya fara shiga. ɗakunan ya-ku-bayi dake ƙasa ne suka fara gamuwa da ambaliyar ruwa.

Jirgin na da hawa uku, wato ‘first class, second class’ da ‘third class’. ‘Third class’ ne can ƙasa, shi ya sa ruwa ya fara mamaye shi.

A lokacin da ya-ku-bayi ke ƙoƙarin haura wa ‘second class’, domin gudun kada su nutse a cikin ruwan su halaka, waɗanda ke can sama a ‘first class’ ba su san me ke faruwa ba, domin su na can su na ta bushasharsu. Wasu da ke ƙoƙarin haura wa zuwa ‘second class’ ba su sami damar yin haka ba, domin an rufe ƙofa da su, saboda kada ruwa ya hauro sama.

Haka nan jirgi ya ci gaba da nutsewa sannu a hankali har sai daga ƙarshe ’yan ‘first class’ su ka gane cewa fa halaka ta zo kusa, kuma cika bakin matuƙin jirgin ya zama na banza. A ƙarshe jirgin ya nutse da akasarin fasinjojinsa walau daga ‘third class, second’ ko ‘first class’.

To, wannan lamari sai ya yi min kamanceceniya da lamarinmu a Najeriya. Mun doshi nutsewa, kuma har wasunmu da dama sun nutse, amma ’yan ‘first class’ ɗinmu, wato ‘elites’ (manya da shugabanni), gani su ke yi kamar komai lafiya, saboda su na can a gidan sama su na facakarsu da morewa. Kuma gani su ke Allah ma bai isa Ya kama su ba, tamkar yadda Edward John Smith ya tsammaci ba zai iya nutsar da Titanic ba.

To, wallahi mu kula, ‘iceberg’ na nan na laluben mu kuma mun tunkare ta, idan mun yi karo, wa ya san waɗanda za su tsira a cikin talakawa da manya? Allah ya kiyaye!

Ali sadiƙ manazarci ne mai lura da harkokin yau da kullum a Nijeriya. Za a iya samun sa a lambar waya kamar haka; 08039702951

By ukarofi