Masoud Pezeshkian ne yayi nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a ƙasar Iran. Masoud ya sami wannan nasarar ne bayan doke abokin hamayyar sa Saeed Jalili.
An ayyana Masoud a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kaso 53.3% na kuri’un da aka kaɗa. Abokin hamayyar shi, ya samu kaso 44.3.Wannan zaɓen shine zagaye na biyu bayan da ba a samu yawan adadin da ake bukata ba na cin zaɓen.
Wannan zaɓen an yi shi ne, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar a wani haɗarin jirgi a watan Mayu. Shugabannin ƙasashe irinsu Rasha, China da Indiya sun taya sabon shugaban murna.
