Ɗan majalisar dokokin Jihar Zamfara ya aurar da marayu 105 da ‘yan bindiga suka kashe iyayensu

Spread the love

Daga Sanusi Muhammad, Gusau

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bungudu da Maru a jihar Zamfara Hon. Abdulmalik Zubairu ya dauki nauyin auren ‘yan mata 105 da ‘yan bindiga suka mayar marayu a mazabar sa.

Da yake jawabi yayin bikin da aka gudanar a garin Bungudu hedikwatar karamar hukumar Bungudu a yau Asabar, Hon. Zubairu ya bayyana cewa manufar shirin shine, a baiwa ‘yan matan damar yin aure cikin sauki.

A cewarsa, kayayyakin da aka bai wa sabbin ‘yan matan da aka aurar da su sun hada da gadaje, cikakkun Katifu, tufafi, saitin Kujeru da kuma kayan dafa abinci.

“’Yan matan sun rasa iyayensu sakamakon harin ‘yan bindiga kuma mun tantance su a hankali don daura masu aure kuma in Allah Ya yarda zan ci gaba da gudanar da shirin a mazabar tawa.” Inji Hon Zubairu.

Ya kuma kara da cewa kowace amarya za a bata Naira dubu hamsin yayin da kowane ango za a bashi Naira dubu dari domin su fara kananan sana’o’i don ciyar da kansu.

A nasa jawabin shugaban taron Sen. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, Sanata mai wakiltar Kano ta kudu ya yabawa Hon. Abdulmalik Zubairu saboda damuwarsa ga al’ummar mazabar sa.

Sen. Kawu ya bukaci sabbin ma’auratan da su kasance masu hakuri da juna tare da jure kalubalen aurensu domin samun iyali masu albarka.

“Batun aure yana bukatar hakuri, sadaukarwa, mutuntawa da fahimtar juna a tsakanin ma’aurata, don haka na roke ku da kuyi amfani da damar da dan majalisar ya baku don tabbatar da dorewar aurenku”. Sen Sumaila yace

By ukarofi