Ƙasar Spain ta samu nasarar doke twakararta ta ƙasar Jamus, wanda sune masu masaukin baƙi. Mikel Merino shine yayi nasarar jefa ƙwallo a cikin ragar Jamus a minti na 119.
Wannan wasan, ya kasance wasa mai zafi da mutane da dama ke ganin dole sai an kai ruwa rana, wanda tabbas wasan ya kayatar matuƙa.
A ɗayan fannin kuma, Ƙasar Portugal tasha kashi hannun ƙasar Faransa a bugun fanereti. Wasan shima ya ƙayatar sosai, tunda aka tashi kunnen doki.
Wannan wasannin sun zama wasa na karshe ga yan wasa Cristiano Ronaldo, Pepe da kuma Toni Kroos daga Jamus.
