Buɗaɗɗiyar wasiƙa kan halifofin sharholiya

Spread the love

Daga NASIR ABDULLAHI GAYAWA

Zuwa ga Dakta Lawi Abubakar Atiku
Unguwar Sanka, Kano
1 ga Yuli, 2024

Assalamu Alaikum,

Wataƙila Maulana ya yi mamakin samun wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa.

Sunana Nasir Abdullahi Gayawa, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano; ɗalibi mai neman digiri na biyu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Houari Boumedeine, Bab Zouer, a Algiers, Algeria.

Na ziyarce ku a birnin Algiers, lokacin bikin tunawa da Shaykh Abdulkarim Al-Maghili, a Disamban 2022 inda muka tattauna abubuwa da dama ciki har da matsalolin da ƴan uwa ke takaicin afkuwar su a ɗariƙarmu ta Tijjaniyya.

Kasa samun ku a waya da rashin ganin amsoshin tambayoyin da na gabatar muku a wancan lokaci, suka tilasta min bin ɓarauniyar hanya don aiko da wannan saƙo.

Ku yi min afuwa, idan na yi kuskure.

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai; Dukkan yabo su tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki; tsira da aminci su tabbata ga Shugaban talikai, Annabi Muhammadu (SAW), da Alayensa da Sahabbansa baki-ɗaya. Muna kara godiyar azurta mu da Allah ya yi da bin turbar salihan bayinSa, managarta, masana, masu aiki da iliminsu, shehunanmu masu riƙo da dokokin ɗariqar Tijjaniyya.

Saboda karantarwar Shehu Ahmadu Tijjani, ba ma cikin masu gararamba ko ɗimuwa a harkokin addini. Mun fahimci yadda za mu bauta wa Ubangiji ta hanyar koyi da Sunnar AnnabinSa (SAW), don gam-da-katar da bayyanar Shehu Ibrahim, ma’abocin Faidhar Tijjaniyya, babban Halifan Shehu Tijjani, mu ke taruwa a harkokin Tijjaniyya.

Hausawa sun ce, “Ranar wanka ba a ɓoyen cibi.” Son zuciyar da wasu khalifofin wannan zamani ke aikatawa, na nutsewa a harkokin ko-in-kula, da sunan wakilcin ɗariƙar da mabiyanta, wanda hakan ya tilasta wa Tijjanawa masu kishin ɗariƙar yin tir gami da Allah-wadai da abubuwan da ke faruwa.

Waɗannan baragurbin wakilai, sun zama tamkar ƴaƴan kuka, don ƙasƙancin da suke jawo wa martabar ɗariƙar Tijjaniyya.

Ƙalubalantar ayyukansu zai hana sauran Musulmi cigaba da yi wa Tijjanawa kuɗin-goro ko bugun ƴan kaɗanya.

Irin waɗannan tsirarun Khalifofi, sun kasance tamkar wake ɗaya a cikin ɗariqar.

Misali, sau da dama maƙiya tafarkin Sufaye na zargin malamanmu da bautar da almajiransu, maimakon sanar da su addini. Tsagwaron gaskiyarsu da ƙoƙarin su fahimtar da mu ilimi da kuma juriyar aiki da shi, ya sa muke yi musu biyayya mai cike da ikhlasi, har wasu ke nuna kishinsu a fili.

A ranar 19 ga watan Yuni, 2024, na haɗu da takardar wani ɗan uwa, Khalifa Yahaya Nuhu Sallau, ta kafofin sada zumunta, inda ya bayyana cewa, muhimman matsalolin Ɗariqar Tijjaniyya da Faidha, a fahimtarsa; sun haɗa da; Yawaitar shehunnan boge; Masu yawon maula da siffar shariftaka; Zakirai ƴan-tamore, masu rawa da birgima da alkafira, wani lokacin har da kiɗan kalangu; Sha’irai masu wuce gona da iri ta furucinsu da yaɗa almara ko tatsuniyoyi a matsayin karamomi da ƙissoshi; Muƙaddamai mata (sayyadodi), ƴan-ci-rani, da masu zantukan soki-burutsu da baragada a addini da sauran su.

Waɗannan rukunan mutane, ba su da wani aiki a kullum sai baza jita-jitar abubuwan da suke illata ɗariƙar Tijjaniyya, kuma korarru a sahihiyar koyarwar Sufanci.

Babban dalilin samuwar wannan koma baya a Tijjaniyya, kamar yadda ya bayyana shi ne, mayar da Khalifanci ya zama kayan gado, mallakin ƴaƴan mamacin shugaba, wanda aka haramta samuwar sa ga almajiransa komai cancantarsu. Wannan son zuciya, yana yi wa kwarjinin ɗariƙar da mutuncinta karan-tsaye a duk faɗin Nijeriya, har da Kano.

Ina fatan za ku yi maraba da wannan buɗaɗɗiyar takarda, a matsayin tunin tambayoyina gare ku, waɗanda har yanzu ina jiran amsoshinsu.

Ta wata fuskar, saƙon da wannan wasiƙa ke ɗauke da shi, kira ne ga shugabanni da mabiya masu kishin ɗariƙar, don mu gudu tare mu kuma tsira tare. Ba ni da wani buri ko manufa saɓanin wannan. Allah ya sani.

Ƴan Ɗariƙar Tijjaniyya, daga ko-ina a duniya, suna ƙaddara birnin Kano, don istiƙamar malamansa da dagewarsu bisa ɗabbaƙa Sunnar Annabi (SAW).

Abin takaici, aka wayi gari da aƙidar fifita Khalifancin gado bisa Khalifancin cancanta, wanda aka gina shi da tubalan fahimtar ilimi tare da aiki da shi, ta zubar da mutuncin mafiya rinjayen zawiyyoyin da aka yi wa ƙarfa-ƙarfar ɗora Khalifofi kan kujerun iyayensu ba tare da suna da cikakken ilimin addini ko gogewa a harkokin mu’amala da zamantakewa ba.

Irin waɗannan Khalifofi, su muridai ke yi wa laƙabi da “kantafi masomin hasara”, saboda rauninsu wajen tafiyar da zawiyyoyinsu masu daɗaɗɗen tarihi, waɗanda manyan malamanmu, mazan-jiya, suka kafa. Na tabbata kowa zai fahimci irin gidajen da nake nufi a garuruwan da Tijjaniyya ke da mabiya, ba sai na ambace su ba.

Sanya ragamar tafiyar da harkokin Tijjaniyya a hannun Khalifofin mun-gada, masu shagala da farautar naman-miya, fiye da yi wa addini da ilimi da ɗariqa hidima, shi ne babban ƙalubalen da ke fuskantar zawiyyoyinmu, fiye da hamayyar abokan adawa, waɗanda muke da kishiyoyin fahimtar addini da su.

Misali, kamar yadda aka sani, kuma zargi ya yi karfi cewar tasirin haƙilon neman abin masarufi da dandazon talaucin aljihu da na zuciya, su suka haifar mana da gurɓataccen Khalifancin Sanusi Lamiɗo Sanusi a Nijeriya. Da yake abokin damo guza, duk da Sanusi ya fifita kujerar sarauta a kan kujerar Khalifancin, irin waɗannan Khalifofi a Kano da sauran jihohin Arewa, a na kyakkyawan zargin cewa sun naniƙe masa a matsayin fadawa, masu rawar jikin ɗaukar umarninsa cikin ladabi da alfahari tamkar bayinsa ko ƙasƙantattun mutane marasa asali.

Saboda rashin cancantar Khalifofin sharholiyar masu riƙe da wakilcin wasu daga cikin manyan gidajen Shehunnan Tijjaniyya a Nijeriya, kamar yadda zargi ya karfafa, an wayi gari hidimar ilimi da koyon ladubban ɗariƙa a waɗannan zawiyyoyin masu tarin albarka da daɗaɗɗen tarihi, sun yi matuƙar rauni.

Ƴan-jabun Khalifofin sharholiya, waɗanda ake zargin ƙorafin a kullum suna bisa wayoyinsu na zamani, don binciken wajen gwamnan wace jiha ko ministan wace ma’aikata ko wane kwamishina ko wace hukuma ko kuma wane hamshaƙin mutum za su kai wa farmaki da sunan wakilcin Tijjaniyya da Tijjanawa.

Abin mamaki, irin wannan yawon karbe-karben da a ke ta yin zargi a kan sa, har ya haifar da zumunci mai qarfi tsakanin Khalifofin sharholiya da wasu malaman qungiyoyin Izala, Wahabiyya, Salafiyya, kasancewar duk kanwar ja ce. Kuma burinsu da manufarsu da kuma muradunsu, sammakal.

Halin da ake ciki, a gidajen wasu manyan Shehunnanmu da suka gabata shi ne, almajiran da suka tumbatsa da ilimi da kamala da alamun tsoron Allah, an zaunar da su a gefe, bakinsu a tsuke. Yayin da ƴaƴan marigayi, waɗanda ilimi bai ishe su ba; na harɗe bisa karagar Khalifancin Zawiyyoyin; suna ta shaci-faɗi da rashin ingantacciyar mahanga. Wannan ne dalilin samun mummunan koma baya da rikirkita a harkokin Shugabancin Tijjanawa a Nijeriya.

Ina cikin mutanen da ba sa ɗebe kyakkyawan zato ga Allah, wurin juya al’amura da kawo gyara, ta hanyoyin da ba a zato ko bakatatan. Don haka, nake shawartar Dattijan Khalifofin da suka rage mana a Kano, masu ilimi da kamala; irin su Shehu Sani Shehu Maihula da Shehu Abdullahi Uwaisu, su fahimci akwai muhimmin aiki jawur a gabansu. Duk da cewa, kawaici da kunya da son zaman lafiya na hana wasu mutane aikata abin da ya fi dacewa, don kawo daidaito a zawiyyoyinmu.

Duk da haka, a matsayin Shehu Sani Maihula, na Shugabancin Majalisar Shura ta Tijjaniyya, ya kamata ya sauke nauyin da ke wuyansa na ƙishirwar a suturta ɗariƙar, a ƙalla a Kano.

Abin alfahari, akwai matasan malamai masu hazaqa da jini a jika jingim, irin su Malam Sanusi Al-Manzawy Arzai, waɗanda idan sun so suna da rawar takawa a jihadin juyo da akalar shugabancin Tijjaniyya tare da saisaita shi bisa tafarki madaidaici.

Illolin da shugabancin zawiyyoyinmu ke fuskanta, bayan rashin ilimi da cancanta, akwai kuma rashin adalci da iya mu’amala ta cikin gida da wajensa, tsakanin ƴan uwa da muridai. Kar fa a manta, Kano ne babban garejin Tijjaniyya a Nijeriya.

Duk wata zawiyya da take buƙatar a yi mata sabis ko garambawul, Kano ake kawo ta. Ko kuma daga Kano ake tura makanikan ɗariqa, ƙwararru, su tayar mata da komaɗa. Ashe kuwa, abin kunya ne a wayi gari ga wasu Khalifofi a Kano a ce birkinsu ya tsinke. Bai kamata mai yi wa wasu kaciya ya girma da loɓa ba.

Mafiya yawan irin waɗannan Khalifofi, wato fadawan Sanusi Lamiɗo Sanusi, idan sun farauto nama da sigar wakilcin Tijjanawa, a cikin jakarsu suke wurga shi; su zuge bakinta, sai sun je ƙuryar ɗakinsu su fito da shi a gasa musu su ci, su kaɗai da matansu da ƴaƴansu. Tamkar mahaifansu waɗanda suke khalifancin, ba su bar kowa a duniya ba, walau almajirai ko zuriya, sai su kaɗai. Na san khalifan da sunansa, a tsakanin almajiran mahaifinsa, Malam Zumbuli, don kwaɗayinsa na abin duniya da baƙar rowa.

Na tabbata irin Khalifofinmu na alaƙaƙai, idan za a sa akwatin zaɓe a zawiyyoyinsu, sannan kuma a yi ƙato-bayan-ƙato; sai sun faɗi wanwar, don baƙin jininsu a wurin ƴan uwansu da almajiran iyayensu. “Ku yi adalci, shi ne mafi kusanci da tsoron Allah.”

Tabbas, naɗin Sanusi Lamiɗo Sanusi, a matsayin babban jagoran Shehunnan boge a Nijeriya, ya bunƙasa harkar Khalifancin ƴan-mun-gada, na sharholiya da bushasha da kuma tsarin kura-tsere-da-na-bakinki. Allah ka kawo mana ɗauki da gaggawa.

A qarshe, ina son jawo hankalin shugabanni da mabiya ɗariqar Tijjaniyya, mu daina yaudarar kawunanmu ta riƙo da Sanusi Lamiɗo Sanusi, a matsayin sahihin Batijjane, kuma jagora a cikin ɗariƙarmu. Mutanen da suka san shi, su ne suke yin mu’amala ta kai-tsaye tare da shi, sun kuma tabbatar da cewa; a irin aƙidarsa, harkokinsa na kasuwanci da kaɗe-kaɗe zuwa bushe-bushen sarauta, su ne kawai a gabansa fiye da komai, fiye kuma da kowa.

Harkokin kishin wannan hanya ta sufaye da ta siyasa da kuma da’awar kishin ƙasa, akwai karfaffen zargi cewar yana yin su ne don nishaɗi da kuma sha’awa kadai, wato kwatankwacin masu wasan karta ko ƙwallon ƙafa ko ludo ko kuma sukuwar doki kawai, don sha’awa.

Misali, lokacin da sojoji suka jefa bom a kan wasu Tijjanawa masu bikin Maulidi, a Ƙauyen Tudun Biri na Ƙaramar hukumar Igabi, cikin Jihar Kaduna, bisa zaton ƴan ta’adda ne, har mutane fiye da ɗari suka rasa rayukansu, a cikin watan Disamba, 2023, mutane da yawa, ciki har da Malaman Izala, irin su Malam Bello Yabo, Sokoto, waɗanda suka zargi gwamnati da kakkausar murya, don bayyana fushinsu da kisan-gillar da aka yi wa Musulmi, “suna cikin harkokin ibadarsu, ba-gaira-babu-dalili.”

Sanusi Lamiɗo bai fito fili ya ƙalubalanci gwamnati, don wannan mummunan aiki ba, balle ya nemi ta biya iyalan mamatan diyya, kamar yadda Malam Bello Yabo; ya yi ta jajantawa cikin fushi da babbar murya. Allah ya saka masa da alheri. Amin.

Abin mamaki, Shehun Izala na tsine wa gwamnati; saboda ta yi aikin ganganci da zaluncin zubar da jinin Tijjanawa a banza, amma Jagoran Ɗariƙar na Boge a Nijeriya, ya yi biris da abin don ba Tijjaniyya ce a gabansa ba. Ba ruwan Sanusi da kare mutuncin milyoyin ƴan Tijjaniyya. Dangantakar Sanusi da Khalifofin Tijjaniyya, kamar manajan darakta ne da leburorinsa.

Misali na biyu, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, 2024, da aka yi bikin tunawa da wani abokin kasuwancin Sanusi Lamiɗo, Mista Herbert Wigwe, a Legas, da Sanusi ya tashi gabatar da jawabinsa, sau uku yana fashewa da kukan rashin da suka yi, duk da cewar ba sa kallon Alqibla daya. Haka Sanusi ya dinga zubar da hawaye: shar-shar- shar, saboda ciwon rabuwarsu. Har yana sambatun bayyana wa gawar:

“Na zaci ni zan riga ka mutuwa, ashe kai za ka riga ni. Wayyo Allah, ba Wigwe”

An gabatar da Sanusi a wurin taron, a matsayin Babban Jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Nijeriya, kuma Sarkin Kano na 14, kamar yadda ma’aikacin Jaridar ‘Daily Trust’, Aliyu Jalal, ya bayyana a rahotonsa na ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024, a cikin jaridar.

Idan mutum ya yi nazarin kalaman Sanusi da ayyukansa, tun lokacin da aka naɗa shi Sarkin Kano da kuma lokacin da aka tuɓe shi, da halin da yake ciki yanzu, a yunƙurinsa na sake ɗare karagar mulki, zai fahimci watakila akwai tazarar gaske tsakanin tunaninsa da nauyin da yake ɗauke da shi na jagorancin al’umma.

Akwai masu zargin cewa, al’adun Sanusi sun fi kama da na sangartaccen mutum mai zaman kansa, maimakon na malamin addini, musamman wai kuma Khalifan Shehu Ibrahim Kaulaha.

Tijjanawa, ga maciji ba a nuna jan-ciki. Mu yi wa kanmu alƙalanci na gaskiya. Mu fahimci, shin wane ne Sanusi Lamiɗo Sanusi? Su waye fadawansa? Idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Alhamdu-lilLahi.

Mai ladabi da neman tabarrukinku,
Nasir Abdullahi Gayawa,
Birnin Algiers, Algeria.

By Babaji