Gamsuwa da gwamnatin Abba ya sa ƙasashaen labarawa suka bai wa al’ummar Kano tallafin ilimi – Sheikh Tijjani Auwalu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MAJITTABA a Kano

Kwamishinan Al’amuran Addini na Jihar Kano Hon. Tijjani Sani Auwalu ya bayyana cewa gamsuwa da yadda gwamnatin Kano ta Alhaji Abba Kabir Yusuf ne musabbabi kuma dalilin da ya sa wasu ƙasashan Musulmi Larabawa kamar irin su Misra, Kuwait, Maroko, Turkiyya, Saudiyya da sauransu, suka yarda su zo, su bai wa gwamnatin Kano tallafin bunƙasa ilimi domin amfanin al’ummar Kano a wannan lokacin.

Bayanin hakan ya fito ne daga baki Sheikh Tijjani Sani Auwalu a lokacin hira da manema labarai a birnin Kano, inda ya ce yanzu haka akwai wata gidauniyya da ake kira Alfijir Foundation wacce gidauniyya ce ta ƙasar Msira ta aminci za ta ɗauki ‘yan asalin Kano yara ƙanana domin, su yi karatun diploma a kan ilimin sanin Alkur’ani da harshen Larabci wanda kuma kyauta ne za su ba da wannan ilimi, duk da ana biyan kuɗi mai yawa ne a wannan makaranta amma gamsuwa da yadda manufofin gwamnatin Kano ya ke akan ilimi ya sa ta amince ta ba gwamnatin Kano wannan dama don amfanin al’umma bisa yadda gwamnatin Abba ta ke tafiyar da al’amura a bayyane kuma cikin taka tsantsan don kyautatawa al’ummar Kano.

Haka zalika ya ce baya ga wannan akwai ƙasar Kuwait wacce ita ma ta yadda ta bawa gwamnatin Kano tallafin ilimi, bisa yarjejeniyyar da ta yi da gwamnatin kano kan wannan al’amari mai muhimmanci haka akwai wata ƙungiya da ake kira World Islamic Link da ta amince za ta gina wata cibiya ta bunƙasa ilimi da kawo cigaba a Kano, wanda kafin wannan lokaci za ta gina cibiyar ne a ɗaya daga cikin jihohin Arewa amma yanzu a Kano za ta gina, haka kuma ƙasashe irin su Moroko, Turkiyya, duk akwai yarjejeniya da aka samu da za su taimakawa gwamnatin Kano wajen bunƙasa harkar ilimi domin cigaban al’ummar Kano.

Haka kuma ya ce idan ka dawo kan maganar gwamnan Kano Abba Kabir za ka ga cewa daga zuwansa aka tura ɗalibai ƙaro karatu karo na biyu a ƙasashen waje har guda 1001 ga kuma biyawa ɗaliban cikin gida kuɗaɗen karatu da kuma zabtare kashi 50 cikin 100 a manyan makarantu mallakar gwamnatin kano ga ware biliyan shida don gina da makarantu a ƙananan hukumomi 44 na Kano, da kamala makarantun sakandire na koyar da addini da gwamnatin injiniyya Rabiu Musa Kwankwaso, gwamna Abba Kabir ya yi alwashin kammala su ba da daɗewa da sauran makarantun sana’o’i suma 44 duk za a kammala nan ba da daɗewa da ikon Allah.

Kwamishinan Addini ya ce tun farkon zuwan sa a matsayin kwamishina ya kai ziyara zuwiyoyin malamai daban-daban na mabambantan ɗariƙu da ƙungiyoyi da sauran su domin neman haɗin kan su, wanda kuma ansamu kyakkyawan haɗin kai a tsakanin malaman Kano ta yadda duk wata matsala daga ta ta so ake warware ta ba tare da wata matsala ba, inda ya ba misali aka samu rashin fahimtar juna da gwamnati da shugaban hukumar Hisbah, aka zauna aka zauna har da ni aka warware abu ya zama tarihi, da dai sauran al’amuran a zaman lafiya a tsakanin al’ummar kano zuwan gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A ƙarshe ya yaba wa gwamnan kan gina aikin gadoji biyu da gwamnatin Kano ta ke yi da sauran ayyuka na tallafawa mata kimanin 500 duk wata da jarin naira dubu 50 har Gwamnan Kano ya kammala mulkinsa, da sai sauran aikin inganta lafiya noma, tsaro, da sauransu duk da ƙalubalen da gwamnatin ta fuskanta farkon zuwanta har zuwa yanzu wanda hakan ba ta sa an samu wani gwamna a arewa ko a Nijeriya da yafi gwamnana kano aiki bai dan kuma da shi akawi a ta bakin kwamishin addini na Kano, ya kuma ce wannan ofishi na ma’aikatar kula da addinai zai ta shitsaye wajen aiki da hukumar zakka domin wayar da kan mawadata su ba da haƙƙin da Allah ya wajabta musu su bayar domin amfanin al’umma mabuƙata, kamar yadda wasu jihohi su ka tsaya tsayin da ka wajen karɓo zakka mai yawa fiye da ta Kano cibiyar kasuwanci.

By ukarofi