Masu kutse sun saci miliyan N329 ta hanyar amfani da lambobin BVN na bogi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu kutse sun saci Naira Miliyan N329 ta hanyar yin amfani da hotunan bogi don yin rijistar lambobin banki na BVN.

Wannan dai na zuwa ne a wani sabon rahoto da Hukumar Kula da Harkokin Hada-hadar Kuɗi ta Nijeriya ta fitar, wanda ta bayyana yadda ake samun yawan damfare-damfare a ɓangaren hada-hadar kuɗi na Nijeriya.

A cewar rahoton, wasu marasa kishin ƙasa da suka yi rajistar BVN ne suka taimaka wa shirin ta hanyar yin rijistar hotunan wasu mutane da suka haɗa da ‘yan Nijeriya da na ƙasashen waje a matsayin waɗanda suka yi rajista kai tsaye.

Daga nan sai aka yi amfani da lambobin BVN wajen buɗe asusu na yaudara a wasu ƙananan bankuna.

Wannan makircin na yaudara ya sa aka yi mu’amalar da ta haɗa da miliyan N329 kwanaki kaɗan bayan da ƙirƙirar lambobin BVN tare da ƙirƙiro asusun bogi.

Binciken ya kai ga goge wasu lambobin BVN da aka ƙirƙira ta hanyar yaudara, kuma an kai rahoton jami’an da abin ya shafa ga jami’an tsaro domin kama su tare da gurfanar da su gaban kotu.

Rahoton ya ƙara da cewa, “Har yanzu hotunan ‘yan Asiya da ‘yan Nijeriya ana ɗaukarsu ana shigar da su BVN ta hanyar yaudara. Ana buɗe asusu tare da waɗannan lambobin BVN.

By ukarofi