Ina zaton zomo ne, inji magidancin da ya kashe ɗansa cikin maye

Spread the love

Wani sabon faifan bidiyo ya bazu a yanar gizo wanda ke nuna wani mutum tatil da ƙwayoyi ya kashe ɗansa ɗaya tilo, lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta.

A cewar faifan faifan bidiyo da ya mamaye dandalin sada zumunta, mutumin yana cikin wani yanayi na maye lokacin da ya kashe ɗansa nasa ɗaya tilo.

Karin bayani a cikin faifan bidiyon sun tabbatar da cewa mutumin ya yi zaton ɗansa nasa zomo a lokacin da ya kashe shi.

Bayan mutuwar ɗan ɗaya tilo, fusatattun mutane sun yi ta dukan mutumin, sun kuma kwatar da gawar yaron a gefen titi.

An sanya wa faifan bidiyo taken; “Cikin mayen shan ƙwayoyi ya kashe ɗansa tilo, lokacin da idanunsa suka nuna masa zomo ne.”

Bayanai sun nuna cewa a halin yanzu mahaifin na gidan yarin

By ukarofi