Mataimakin shugaban ƙasar Brazil da matarsa sun iso Nijeriya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Mataimakin shugaban ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin tare da matarsa Maria Lúcia Alckmin, sun sauka a safiyar Talata a sashen na musamman a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Ziyartar na da nufin halartar zaman na biyu na tsarin tattaunawar dabarun haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Brazil (SDM), wanda ake sa ran zai kawo sauyi a dangantakar ƙasashen biyu.

An tarbi tawagar Brazil ɗin ne daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia; ministar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr. Jumoke Oduwole; ministan raya kiwo, Idi Mukhtar Maiha; da ministan noma da tsaron abinci, Sanata Abubakar Kyari. Sanata Hadejia ya bayyana ziyarar a matsayin muhimmiyar dama a ƙoƙarin Najeriya na farfaɗo da tattalin arziƙi ta hanyar sabbin haɗin gwiwa da ƙasashen kudu.

Taron, wanda zai ɗauki kwana uku, zai ƙare da sa hannun yarjejeniyoyi sama da 30 a fannoni daban-daban, ciki har da haɗin gwiwar tsaro, canja fasahar noma, makamashi, da musayar al’adu. Najeriya na fatan amfani da ƙwarewar Brazil a fannin noma da masana’antu domin cika burin tsarin “Sabon Fata” da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.

By ukarofi