Zanga-zanga ta ɓarke a jami’ar IBB bayan ‘yan fashi sun kashe ɗalibi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wasu ƴan fashi da makami sun kashe wani ɗalibi a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai, da safiyar Litinin, bayan sun kai hari wani ɗakin kwana na ɗalibai da ke unguwar Ndakikpabu. Ɗalibin da aka kashe mai suna Abdulwahab Abubakar, ɗalibi ne a ajin ƙarshe na Chemistry Education a Faculty of Education.

Rahotanni sun bayyana cewa an soka Abdulwahab wuka a wuya da misalin ƙarfe 3 na safe a gidansa na wajen harabar jami’a. Duk da an garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati na Lapai, an tabbatar da rasuwarsa nan take. Wannan lamari ya tayar da hankalin ɗalibai, inda suka fito kan tituna domin nuna fushinsu kan rashin tsaro.

Ɗaliban sun toshe hanyar Agaie–Lapai tare da zargin jami’ar da gazawa wajen kare rayukan ɗalibai. Wasu daga cikin su sun lalata ofishin tsaro na jami’ar, sannan wasu sun kutsa fadar Sarkin Lapai domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu.

Ɗaya daga cikin ɗaliban, Mohammed Hassan, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko ba, inda a makon da ya gabata ma aka kai hari kuma aka yi wa wasu ɗalibai mata fyade.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin mai magana da yawunta, SP Wasiu Abiodun, inda ya ce tuni aka aika da jami’an sintiri zuwa yankin don dawo da zaman lafiya. Ya kuma tabbatar da cewa an fara bincike tare da bada umarni daga Kwamishinan ‘yan sanda cewa sai an kamo masu laifin an hukunta su.

Jami’ar dai ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da faruwar lamarin a lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi