Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Wakilai ta sanar da rasuwar Mataimakiyar Mai Tsawatarwarta, Adewunmi Oriyomi Onanuga, mai wakiltar mazaɓar Ikenne/Sagamu/Remo ta Arewa a Jihar Ogun.
A cewar mai magana da yawun Majalisar, Ɗan majalisa Akin Rotimi Jr, ƴar majalisar ta rasu ne a ranar Laraba bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.
A sanarwar da Rotimi Jr ya fitar, an haifi ƴar majalisar ne a ranar 2 ga watan Disambar 1965, wadda ta kasance mai jajircewa da wakilci na gari ga al’ummar mazaɓarta.
An fara zaɓar ta ne a shekarar 2019 a ƙarƙashin inuwar jami’yya mai mulki ta APC inda ta yi aiki a matsayin Shugabar Kwamitin Harkokin Mata da Ci-gaban al’umma a majalisar tare da jagorantar shirye-shirye na inganta mata da bunƙasa harkokin kula da al’umma.
A lokacin da aka sake zaɓar ta a shekarar 2023 ne, sai ƴar majalisar ta samu muƙamin Mataimakiyar Mai Tsawatarwa inda ta bayyana jagoranci na musamman gami da jajircewa wajen ladabtarwa a yayin zaman majalisa.
Majalisar ta kuma aika da saƙon ta’aziyya gami da jajenta wa iyalan marigayiyar da abokan arziƙi da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Ogun musamman ƴan mazaɓarta.
Sanarwar ta ƙara da cewa, iyalanta za su sanar da lokacin jana’izarta a lokacin da ya dace.
Har’ilayau, Majalisar ta kuma yi mata addu’o’i na gari da kuma fatan kayawawan ayyukanta su cigaba da tasiri a zukatan al’umma.