Matar Bahaushe

Daga BASIRA SABO NADABO

Matar bahaushe manyan duniya, ba a ɗaukar wankan kece raini sai za a yi tafiya gidan biki, mijinki ya iske ki da ɗaurin ƙirji.

Matar bahaushe mai abin mamaki, a baki kuɗin cefane masu yawa ki yi girki da rabi ki kai rabi gidan mai adashi.

Matar bahaushe ɗakinki kamar wajen siyar da dila, banɗaki kamar na kuturwa, mawankinki kamar kantin siyar da kwanonin abincin masu datti, ba kya sharar ɗaki sai an ji ƙawaye za su kawo ziyara saboda kar su raina ki.

Matar bahaushe sai kin gama shirin zuwa wajen biki za ki tambayi mijinki, a hana ki zuwa an taɓo bala’i.

Matar bahaushe mijinki na hanya za ki kama hanya ki shiga maƙota yawon gulma, ya dawo ya yi faɗa ki ce ai ya daina son ki.

Matar bahaushe kullum kina zaune dagaja-dagaja babu ruwanki da gyara sai an tashi yi miki kishiya sai ki fara zancen ai ya daina son ki.

Matar bahaushe kina zaune saman kujera mijinki ya dawo daga aiki babu sannu da zuwa balle ga ruwan wanka, ke dai kina zaune kina WhatsApp ko Facebook da ƙawayenki kina ƙyalƙyala dariya.

Matar bahaushe babu kalamai masu daɗi da za ki roƙi miji kuɗi ya ce ba shi da shi ki ce ya hanaki ai ga shi can yana ba kishiyarki kullum ke ce cikin zargi.

Matar bahaushe ba kya kwalliya da mijinki ya yi kwalliya ki ce za shi zance.

Matar bahaushe ke ce dai wacce ba ta iya girki mai daɗi haɗe da nau’ukan lemuka masu garɗi.

Matar bahaushe ce ba ta juya biyar ta zama goma amma duk bikin ‘yan’uwa da ƙawaye ki ce sai an miki.

Matar bahaushe ce mai rainuwa da rashin godiyar samun miji.

Matar bahaushe ke ce ɗin dai dangin miji suka daina zuwa wurinki saboda rashin tarba mai kyau.

Matar bahaushe ke ce ɗin nan da kike zama silar rayuwar mijinki.

Matar Bahaushe:

Matar bahaushe ‘yar aljanna ba a ba ki kuɗin cefane ba amma ki yi girki mai daɗi har da nama zuƙu-zuƙu da kuɗin da kika samo da kika je gida.

Matar bahaushe saliha kina zaune mijinki yana charting da ‘yan’mata in kika nufo shi ya ce bai son fitina.

Matar bahaushe ba tare da kin yi masa komai ba zai yi miki kishiya, amma babu kalamai masu daɗi balle kayan dannan ƙirji sai dai ya ce in kin ji za ki iya ki zauna don aurena babu fashi.

Matar bahaushe ba a saya miki sabulu ba amma a ce ba kya tsafta ki zauna da datti ya kira ki da ƙazama, in kika ce babu sabulu a ce ina wanda aka kawo watan da ya gabata.

Matar bahaushe kina son mijinki ya yi miki kwalliya amma bai yi sai dai ya zauna kullum da jallabiya ko kuma gajeran wando kamar ɗan kokawa.

Matar bahaushe kina son wasa da dariya amma kullum fuskar mijinki kamar ta shanu.

Matar bahaushe ce kullum kina yawon ɗibo ruwa shi kuma yana zaune a majalisa yana ƙirga wucewar matan mutane.

Matar bahaushe ita ce wannan salihar da kodayaushe ta ke nasiha ga mijinta.

Matar bahaushe ce kullum gidanta yana cikin ƙamshi amma da mijin bahaushe ya shigo ya ce gidan na ƙauri.

Matar bahaushe ce aljannarta ke gabanta ba ƙuntatawar miji ba, ita ce ɗin nan dai ta ke kamuwa da bugawar zuciyar da zai yi sanadiyyar rayuwarta saboda haƙuri da halayyar mijin bahaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *