Manufar Gwamnatin Tarayya na samar da Dala Tiriliyan 1 na tattalin arzikin ƙasa ba zai yiwu ba idan har aka cigaba da samun taɓarɓarewar matsalar rashin tsaro a ƙasar. Mafita ita ce jami’an tsaro su gaggauta ɗaukar mataki tare da tabbatar da cewa an fatattaki ’yan bindiga da sauran miyagun da ke ta’addanci a ƙasar. Shugaba Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin leƙen asiri a wani taron tsaro da shugaban ƙasa ya gudanar kwanan nan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
A cewar shugaban, yayin da ake samun cigaba tare da kawar da wasu matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, a ƙarshe dai za a ayyana nasara ta hanyar kawar da barazanar rashin tsaro bakiɗaya ga ‘yan ƙasar. Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babban ƙalubale a ɓangaren ƙoƙarin da gwamnati ke yi na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
Shugaban ya kuma jaddada cewa dole ne sojojin ƙasar su cimma burinsa na ganin cewa al’ummar ƙasar sun samu cigaba mai ɗorewa na samar da ganga miliyan biyu na ɗanyen mai a kowace rana, ciki har da na’urar dakon man fetur a cikin rubu’in farko na shekarar 2024.
Kalaman na Tinubu na zuwa ne a ranar da ’yan ta’adda suka kashe aƙalla mutane 17 tare da yin garkuwa da wasu 58 a wasu ƙauyuka uku da ke ƙaramar hukumar Kauru ta Jihar Kaduna; da wasu da ake zargin ’yan ƙungiyar Boko Haram ne sun kashe wani fasto na Cocin Christ In Nations (COCIN) a garin Kwari da ke ƙaramar hukumar Geidam a Jihar Yobe a wani sabon barazanar ‘yan bindiga da ya ɓarke a sassan ƙasar nan.
Hakazalika, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Bwari da ke babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi awon gaba da mutane bakwai ‘yan gida ɗaya tare da kashe ɗan sanda guda. Rikicin ya ƙara nuna damuwa da rashin tsaro a Abuja da sauran sassan ƙasar.
Babu shakka, rashin tsaro ya zama hatsari a halin yanzu ga ‘yan Nijeriya da tattalin arzikinta. Hasashen kan tattalin arzikin ƙasar daga masana da hukumomin ƙasa da ƙasa, abin ya yi muni. Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) a cikin rahotonsa na ‘World Economic Outlook Update: Near-Term Resilience, Persistent Challenges (Yuli 2023)’, ya yi hasashen cewa cigaban tattalin arzikin Nijeriya zai ragu a 2023 da 2024 saboda matsalolin tsaro a fannin mai. Ta bayyana cewa, tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 3.2 a shekarar 2023, kafin ya ragu zuwa kashi 3.0 a shekarar 2024.
IMF ta ce, “A yankin kudu da hamadar Sahara, ana hasashen cigaban zai ragu zuwa kashi 3.5 cikin 100 a shekarar 2023 kafin ya kai kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2024. Ana hasashen cigaban Nijeriya a 2023 da 2024 sannu a hankali zai ragu, daidai da hasashen watan Afrilu, wanda ke nuna taɓarɓarewar al’amuran tsaro a fannin mai.”
An riga an fara ganin tasirin rashin tsaro, cin hanci da rashawa da sauran munanan abubuwa masu ban tsoro yayin da sama da kamfanoni 15 na ƙasa da ƙasa suka bar Nijeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, a cewar bayanai daga ƙungiyar tuntuɓar ma’aikata ta Nijeriya (NECA).
A wasu sassan ƙasar kuma, rashin tsaro ya gurgunta harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma. A shiyyar Arewa ta tsakiya manoma ba za su iya zuwa gonaki ba saboda rashin tsaro. Hakan ya haifar da ƙarancin kayan abinci da tsadar kayan masarufi na gida. Rashin tsaro ya yi matuƙar ga samuwar jari daga waje kai tsaye. Yayin da kamfanoni da yawa ke barin ƙasar, ma’aikata da yawa suna rasa ayyukansu, kuma yawancin ‘yan ƙasa suna shiga cikin matsanancin talauci.
Jaridar Blueprint Manhaka na ganin cewa bai kamata a bar lamarin ya cigaba ba. Bai kamata Shugaban ƙasa ya tsaya kawai yana ƙorafin rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa ba. Ana buƙatar yin wani abu mai tsauri kuma cikin gaggawa don daƙile barazanar. Yakamata a ƙarfafawa jami’an tsaro ƙwarin gwiwa tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin murƙushe masu hannu a cikin matsalar rashin tsaro. Babban aikin gwamnati shi ne samar da tsaro da jin daɗin jama’a. Bai kamata gwamnatin tarayya ta rungume hannuwa ba. Wannan lokaci ne da za a murƙushe ’yan bindiga, ’yan ta’adda da sauran miyagun da ke addabar ’yan ƙasa.