Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ta gudanar da taron gaggawa a sakatariyar ƙungiyar da ke Abuja a daren Laraba, inda Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaron Ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya halarci taron.
Duk da cewa an hana ’yan jarida su ba da labarin buɗe taron, ajandar da aka raba wa gwamnonin sun nuna cewa batutuwan da suka shafi harkokin tsaro na jihohi da na ƙasa ne zai sa a gaba a tattaunawar.
Sauran abubuwan da aka jera domin tattaunawa sun haɗa da tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya cire, da nazari kan ajandar majalisar zartarwa ta ƙasa, da taƙaitaccen bayani kan sabuwar dokar samar da wutar lantarki.
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ne ya jagoranci taron.
Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Babagana Zulum na jihar Borno, Hope Uzodimma na jihar Imo, Ademola Adeleke na jihar Osun, Chukwuma Soludo na jihar Anambra, da Alex Otti na jihar Abia da dai sauransu.
An sake ƙara nuna damuwa kan sha’anin tsaro a ƙasar bayan kashe aƙalla jami’an soji 36 da suka haɗa da manyan hafsoshi a baya bayan nan da wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne suka yi a Kundu ta hanyar Zungeru a Ƙaramar Hukumar Wushishi ta jihar Neja.
A wata ziyarar da ya kai wa sojojin a jihar Neja a ranar Laraba bayan harin ‘yan bindigar, babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ja hankalinsu da kada su bari hankalinsu ya tashi, sai dai su kare Nijeriya da kwato sararin da ke hannunsu a halin yanzu, da kuma kawar da ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a sassan ƙasar.