Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Manyan hafsoshin dakarun ECOWAS sun ce a shirye suke su tura sojoji, don mamaye Nijar da nufin dawo da mulkin dimokuraɗiyya a faɗin ƙasar.
Bayan da jami’an tsaron shugaban Ƙasar suka karɓe mulki daga hannun shugaba Mohamed Bazoum, ƙungiyar ECOWAS ta bada wa’adin kwanaki 7 ga sojojin ƙasar da su maido da shugaban ƙasar ko kuma su fuskanci takunkumi, ciki har da yiwuwar ɗaukar matakin soji.
Sai dai gwamnatin mulkin sojan ta yi kunnen uwar shegu kan maganar ECOWAS ta kuma yi tir da tsoma bakin ƙasashen waje.
Bayan haka, ƙungiyar ta yankin ta buƙaci hafsoshin tsaro na ƙungiyar mai mambobi 15 da su fara aiki da rundunonin tsaro.
A wani taro da aka yi a Accra, babban birnin Ghana a ranar Alhamis, hafsoshin tsaron qasar sun ce sun shirya tsaf domin dawo da mulkin farar hula a Nijar.
A cewar gidan talabijin na Aljazeera, dukkan ƙasashe mambobin ƙungiyar in ban da waɗanda ke qarqashin mulkin soja da kuma Cape Verde sun yi alƙawarin shiga cikin shirin.
An ruwaito kwamishinan ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana haka.
Jaridar ta ƙara da cewa, babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya ce, “Dimokraɗiyya ita ce abin da muka tsaya a kai, kuma ita ce abin da muke ƙarfafawa.
“Manufar taronmu ba wai kawai mu mayar da martani ne ga abubuwan da suka faru ba, amma don tsara tsarin da zai haifar da zaman lafiya da inganta zaman lafiya.”
Burkina Faso da Mali, waɗanda suka fuskanci juyin mulki da dama tun daga shekarar 2020, sun yi gargaɗin cewa duk wani tsoma bakin soja a Nijar za a ayyana shi a matsayin wani yaƙi, wanda ke nuna karayar da ake samu a yankin tsakanin ƙasashenta da ke gaɓar teku da kuma na yankin Sahel mai fama da rikici.