Sojoji 36 ‘yan bindiga suka kashe a Neja – Hedikwatar Tsaro

Daga BASHIR ISAH

Hedikwatar Tsaro (DHQ) da ke Abuja ta bayyana cewa, sojoji 36 ‘yan bindiga suka kashe a Jihar Neja.

A ranar Lahadin da ta gaba ‘yan bindiga suka yi wa sojoji kwanton-ɓauna a hanyar Zungeru zuwa Tegina inda suka kashe sama da sojoji 20.

Sai dai mai magana da yawun babban ofishin tsaro na ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, ya ce askarawa 36 ne suka mutu a harin.

Buba ya bayyana haka ne a wajen taron manema labarai na mako-mako da ya shirya inda ya yi ƙarin haske game da adadin sojojin da ‘yan bindigar suka kashe da kuma aikin kwashe tarkacen jirgin saman soji mai saukar ungulu da ya yi hatsari a jihar ranar 14 ga Agusta, 2023.

Da yake amsa tambaya gane da abin da ya haifar da hatsarin jirgin, Buba ya ce bincike na kan gudana a kan batun don gano haƙiƙanin abin da ya haifar da shi.

Daga nan, jami’in ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su yi watsi farfagandar ‘yan bindiga kana su ci gaba da kasancewa masu kishin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *