Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ɗage shari’ar zargin wawushe N6.9bn kan Emefiele

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja, ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar sabon zargin da Gwamnatin Tarayya ke yi wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, na yin sama-da-faɗi da kuɗin gwamnati Naira biliyan 6.9.

A ranar Alhamis aka gurfanar da Emefiele tare da wata Sa’adatu Yaro da kamfaninta mai suna April1616 Investment Limited bisa zargin laifuffuka 20 da suka haɗa da haɗin baki, amfani da haramtattun damammaki da sauransu.

Laifukan da aka ce sun saɓa wa Sashe na 19 na Dokar Laifukan Rashawa da Dangoginsu na Dokar 2000.

Sai dai zaman shari’ar ya gamu da tsaiko sakamakon rashin bayyanar mai kare kai na biyu, wato Sa’adatu Yaro.

A cewar lauyan Sa’adtu, wadda yake karewa ba ta samu zuwa kotun ba ne saboda rashin lafiya.

Daga nan, Alƙalin Kotun, Muazu Hamza, ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 23 ga Agusta.