Daga BASHIR ISAH
Ya zuwa ranar Litinin ta makon gobe idan Allah Ya kai mu ake sa ran Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai rantsar da sabbin ministocinsa da ya naɗa.
Sanarwar da ta fito ta bakin Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ta ce bikin rantsarwa zai gudana ne a babban zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 10 na safe.
Sanarwar ta ƙara da cewa ‘yan rakiya biyu-biyu kacal aka amince wa ministocin su take musu baya zuwa wajen taron.
“Ana sa ran ministocin kowanne ya zo da ‘yan rikiya guda biyu.
“Sannan duka ministocin da sauran baƙi kowa ya kasance a mazauninsa da misalin ƙarfe tara na safe,” in sanarwar.
Waɗanda za a rantsar ɗin sun haɗa da:
Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani – Bosun Tijani
Ƙaramin Ministan Muhalli – Ishak Salaco
Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki – Wale Edun
Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki – Bunmi Tunji
Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu
Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma – Tunji Alausa
Ministan Ma’adinai – Dele Alake
Ministan Yawon Buɗe-Ido – Lola Ade-John
Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola
Ministan Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite
Ministan Wasanni – John Enoh
Ministan Abuja – Nyesom Wike
Ministar Al’adu – Hannatu Musawa
Ministan Tsaro – Muhammad Badaru
Ƙaramin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
Ƙaramin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sununu
Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Ahmed M. Dangiwa
Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Abdullah T. Gwarzo
Ministan Kasafi da Tsare-Tsare – Atiku Bagudu
Ministan Muhalli (Kaduna)
Ƙaramar Ministar Abuja – Mairiga Mahmud
Ministan Albarkatun Ruwa – Bello M. Goronyo
Ministan Noma da Samar da Abinci – Abubakar Kyari
Ministan Ilimi – Tahir Maman
Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’Idu A. Alkali
Ministan Harkokin Waje – Yusuf M. Tuggar
Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a – Ali Pate
Ministan Harkokin ‘Yan Sanda – Ibrahim Geidam
Ƙaramin Ministan Ƙarafa – U. Maigari Ahmadu
Ministan Ƙarafa – Shuaibu A. Audu
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai – Muhammed Idris Malagi
Ministan Shari’a – Lateef Fagbemi
Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Simon B. Lalong
Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida – Imaan Sulaiman-Ibrahim
Ministan Ayyuka na Musamman – Zephaniah Jisalo
Ministan Albarkatun Ruwa – Joseph Utsev
Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci – Aliyu Sabi Abdullahi