Ingantaccen rubutu shi ke kai marubuci ko’ina a duniya – Rahmatu Lawan

“Manhajar Hikaya ba ta ɗora littattafan batsa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Masu bibiyar wannan shafi na Adabi muna yi muku fatan alheri a kodayaushe. Kamar kowanne mako, yau muna ɗauke ne da wata tattaunawa da muka yi da Hajiya Rahmatu Lawan Ɗalha, wata ƙwararriya a harkar sarrafa fasahar sadarwa wacce ita da mijinta masanin fasahar zamani suka samar da Bakandamiya Hikaya, wasu tagwayen manhajoji da ke ba da gudunmawa ga cigaban rubutun adabi da rayuwar marubuta.

Ɗaya manhaja ce ta ƙarfafa zumunci tsakanin marubuta da masu karatun littattafansu, sai kuma manhajar tallata littattafai da rubuce-rubuce na ilimi. A tattaunawar da wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya yi da shugabar gudanarwar wannan manhaja ya gano dalilan da ya sa waɗannan ma’aurata masu hikima da jajircewa, suka yanke shawarar ɓullo da wannan fasaha da ta bambanta da sauran fasahohi irinta.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

HAJIYA RAHMATU: To, Assalam Alaikum. Da farko dai ina farinciki da kuma miƙa godiya da wannan dama da ku ka bani a madadin Bakandamiya. Sunana Rahmatu Lawan Ɗalha. Ni matar aure ce, sannan ina da yara. Ni ce shugabar sashin kula da ayyuka na kamfanin manhajar Bakandamiya, kuma ɗaya daga cikin mambobin gudanar da manhajar Bakandamiya da Hikaya, waɗanda aka samar don inganta harkokin rubuce-rubucen adabi.

Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihinki da matakin da ki ke a rayuwa?

An haifeni a garin Jalingo na Jihar Taraba kusan shekara arba’in da suka wuce. Sunan mahaifina Alhaji Muhammad Maiharka, sannan sunan mahaifiyata Hajiya Fatima. Na yi makarantar firamare, da sakandire, na kuma koyi aikin malanta a Kwalejin Ilimi ta Jalingo. Na tava aikin koyarwa kuma, na shekara biyu a wata ƙaramar sakandire ta Mafindi da ke nan Jalingo. Na fara karantar ilimin Tsumi da Tanadi (Economics) a Jami’ar Jihar Taraba har na tsawon shekara ɗaya, amma ban kammala ba sai maigidana ya samu aiki a Saudi Arabia, wannan ya sa muka koma da zama a can tun 2011.

A can Saudi Arabia na sake samun damar komawa makaranta inda ya shiga fannin nazarin ilimin sarrafa hanyoyin sadarwa (MIS) a Jami’ar Yanbu University College dake birnin masana’antu na Yanbu Industrial City a yankin Al-Madina Province. Kuma Alhamdulillah a nan na kammala karatuna na digiri na farko, wato Bsc. Na ɗan yi wasu ƙananan aikace-aikace a can Saudi Arabia, amma saboda tsauraran dokokin ƙasar da kuma yanayin karatu da iyali ban yi nisa sosai ba.

Na fara aiki da Bakandamiya tun kafuwarta a shekarar 2016, a matsayin mai kula da gudanar da manhajar, kuma har zuwa yanzu da nake riqe da shugabancin sashin gudanar da ayyukan kamfanin bakiɗaya.

Ba mu labarin kafuwar kamfanin Bakandamiya da Hikaya, me ya haɗa su kuma me ya raba?

Labarin kafuwar kamfanin Bakandamiya labari ne da ya samo asali daga irin burika da sha’awar da maigidana, Malam Lawan Ɗalha, ke da su na son ganin cigaban Arewa, Nijeriya da ma Afirka bakiɗaya. An ƙirƙiro da wannan manhaja ta Bakandamiya ne wani lokaci cikin 2016, domin cimma wannan manufa tasa.

An yi amfani da tsarin sadarwa na ‘social software’ wajen ƙirƙiro da wannan manhaja ne saboda haka Bakandamiya na aiki ne kamar yadda manhajar Facebook ke aiki. Sannan wani ƙarin burgewa kuma shi ne an yi wa manhajar tsarin amfani da harshen Hausa ne.

Alhamdulillah, Cikin ƙaramin lokaci mun haɗa mambobi sama da dubu biyar. Wani abu da muke yi wanda ya sha bambam da irin su Facebook shi ne muna wallafa maqalu masu inganci a fannoni daban-daban, kamar su kimiyya, zamantakewa, fasaha, girke-girke da sauransu.

Muna da gefen bidiyo, inda muke wallafa bidiyo a kan amfani da fasahar zamani da sauran abubuwa da suka shafi kimiyya da fasaha. Akwai sashen haɗa sauti, kamar podcast haka shima yana da vangarori mabambanta na ilimi. Muna da gefen hotuna zalla domin saka hutunan tarihi da na shahararrun mutane. Muna da sashen buɗe zauruka (groups) don mutane masu ra’ayoyi iri ɗaya da sauransu.

To, a fannin zauruka, akwai zaurukan marubuta daban-daban, inda muka lura suna gaba-gaba a cikin duk vangarori da muke da su na Bakandamiya, ba don komai ba, sai don kishin su akan abin da suka sa a gaba, wato rubutu da harkar adabi. Ana cikin wannan tafiya tamu da marubuta mai ban sha’awa, sai muka shirya wata babbar gasar muhawara, wadda muke kyautata zaton ita ce irinta ta farko a harkar adabi a Arewa.

Kwatsam, sai kuma muka samu wata matsala a na’urar da muke gudanar da ayyukan manhajar tamu ta Bakandamiya, wanda zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin mu daidaita gyaransa. Dalilin wannan ya sa muka fara tunanin wani abu da zai maye wannan muhimmin gurbi na alaqa tsakaninmu da marubuta, daga ƙarshe shi ya haifar da buɗe manhajar Bakandamiya Hikaya.

Bakandamiya Hikaya, taska ce ta zallar harkokin rubuce-rubucen adabi, kama daga littattafan hikaya na zube, na wasan kwaikwayo, da waƙoƙi, da kuma rubutun maƙalu, wato babban tsari ne na bunƙasa harkokin ƙirƙira. A taƙaice, wannan shi ne tarihin kafuwar Bakandamiya da kuma alakar Bakandamiya da Hikaya, ko in ce Bakandamiya Hikaya.

Waɗanne manufofi ne suka haifar da kafuwar wannan manhaja, kuma wanne tasiri take samu?

Manufofin Bakandamiya Hikaya sun haɗa da, bunƙasa harkokin marubuta, da rubutunsu. Misali, saɓanin sauran kafofin buga labari wanda kawai marubuci zai je ya saka rubutunsa ne babu wadda zai duba ko ba shi shawara, a Bakandamiya Hikaya, duk rubutun da aka ɗora sai editocinmu sun duba kafin a sake, duk da cewa yawan rubutun da ƙarancin editocin ya sa ba ma iya dubawa kamar yadda muke buƙata a halin yanzu.

Sannan abu na biyu, don haɗa kai da taimakawa marubutan wajen ganin suna cin gajiyar basirarsu da Allah (SWA) Ya basu ta rubutu, waxannan marubuta kuwa sannanu ne ko masu tasowa. Da yawa marubuta masu basira da za su amfani al’umma sun bar harkar rubutu saboda rubutun ba ya iya samar musu ko kuɗin da za su sayi kayan rubutun bare na sayen data ko dan tafiye-tafiye da za su yi don yin bincike su inganta aikinsu.

Sannan a ɓangaren makaranta kuma, Bakandamiya Hikaya ta samar musu wajen samun duk irin labaru da rubuce-rubucen da suke so na marubuta daban-daban a taskance, wuri guda, cikin ingantaccen rubutu, sannan kuma su karanta su da kuɗi yan kaɗan. Amfanin rubutu ba kawai isar da labari ko saƙo ba ne, suna da muhimmanci wajen inganta ilimin harshe da adana tarihi da al’adun al’umma.

Kowa ya san irin taɓarɓarewa da ƙa’idojin rubutu har da tarbiyya da aka samu a dalilin yaɗuwar fasahar zamani wanda ya bawa kowa dama ya rubuta abin da ya ke so da irin kalar rubutun da ya ke so, ya watsa shi a inda yake. Muna fata idan aka cigaba da tafiya da samun haɗin kan marubuta da waɗanda abin ya shafa, in sha Allah Bakandamiya Hikaya na nufin ba da gagarumar gudummawa don kawar da irin wannan karan tsaye da ake wa rubutu da adabi, musamman a Arewacin Nijeriya.

Yaya ku ka yi nazarin kasuwancin littattafai a hanyar yanar gizo?

Kasuwancin littattafai ta yanar gizo kasuwanci ne da sauyin zamani ya kawo mana, wanda a nazarinmu, yana da tasiri ƙwarai da gaske. Saboda yanar gizo ta bamu damar yaɗa littattafai wanda duk duniya ake samu cikin ƙanƙanin lokaci. To, amma kuma cikin wannan cigaban akwai qalubale da dama, kamar satar rubutun a ɗora kan wata taska ko wani shafi a zaurukan sada zumunta ba tare da sanin masu haƙƙin mallaka ba, da sauransu.

Kawo yanzu kun fara fahimtar ribar da za ku samu idan marubuta sun rungumi wannan sabon tsarin da kyau?

Alhamdulillah, muna da yaƙinin cewa wannan harkar za a ribace ta sosai idan marubuta da makaranta sun rungumeta yadda ya kamata. Wannan ribar kuma daga marubuta har mu masu manhajar zai shafa.

Mene ne ya bambanta tsarin manhajar Hikaya da sauran manhajoji na tallata littattafai irin su Okada Books da Arewa Books?

Banbancin Bakandamiya Hikaya da sauran masu wallafa littattafai a yanar gizo musamman na ɓangaren Hausa/Africa shi ne, mu sayen littafi muke yi daga wajen marubuci sannan mu bai wa editoci su duba don ƙara inganta rubutun kafin mu buga. Har ila yau, mu ne ke ɗaukar ɗawainiyar tallata littattafan kusan kaso tamanin zuwa tamanin da biyar cikin ɗari.

Amma sauran takwarorinmu, marubuci shi zai ɗora kayansa, da buƙatar gyara ko babu, kuma a duk yadda ya ɗora haka nan za a sake shi, daɗin daɗawa shi zai tallata kayansa. Gaskiya mu a ɓangarenmu muna muhimmanta inganci da nagartar rubutu fiye da komai, domin adabi shi ne ginshiƙin ilimi, tarihi da taskace al’adun al’umma, kuma ka ga bai kamata a yi wasa da hakan ba, ko kuma a fi muhimmanta ɗan ribar kuɗin da za a samu a kan ciyar da al’umma gaba.

Wacce riba marubuci zai samu ta hanyar sanya littafin sa a kasuwar onlayin, musamman a Hikaya?

Kamar yadda na faxa a baya, mu a Bakandamiya Hikaya muna sayen littattafai ne, amma muna da qa’idar sayen littafi, kamar misali duk wani sabon marubuci idan ya zo zaisaka littafin shi a wajen mu to, muna buƙatar ya saka mana na free tukunna, wanda mu ma a ɓangarenmu a free muke barin irin waɗannan littattafan – sai dai ba mu saka littattafan kyauta a ɓangaren na kuɗi.

Dabaran yin hakan shi ne makaranta su fara sanin irin labarunka da irin salon rubutunka. To, ribar a nan shi ne, idan marubuci da gaske yake yi to, lallai ba jimawa za mu fara sayen littafinsa kuma mu ba shi kuɗinsa ba tare da ya yi ta fama da masu satan rubutu ko tallatawa ba. Kuma ba na zaton akwai wurin da ake sayen littattafai kamar yadda muke saya.

Wasu daga cikin matsalolin da ake ganin ana samu da wasu marubuta shi ne rashin bin qa’idojin rubutu, da kuma masu rubutun batsa, waɗanne ƙa’idoji ku ka sa da za su magance waɗannan matsalolin?

Lallai maganar ƙa’idodjin rubutu babbar matsala ce da muke fuskanta a wannan fanni. Mu a Bakandamiya Hikaya mun ɗauki matakai ƙwarara na magance ko rage wannan matsala. Matakai kamar sanya ƙwararru suna mana rubutu akan waɗannan maudu’ai na ƙa’idojin rubutu da sauran fannonin adabi. Yanzu haka idan ka duba gefen Taskar (blog) Bakandamiya Hikaya za ka tarar muna da maƙalu masu yawa waɗanda manazarta da malaman kwalejoji da jami’o’i suka rubuta a wannan fanni. Wani mataki kuma shi ne na shirya taron bita domin karantar da marubuta. Mun taɓa shirya irin wannan bita a baya wanda Malam Danladi Haruna ya jagoranta, kuma muna da shirye-shire na musamman don cigaba da yi.

Yanzu haka muna da wani shiri na musamman don koyar da marubuta to, amma ba zan so na yi bayaninsa ba sai ya bayyana in sha Allahu. Sannan duk murubucin da ya ɗora littafinsa sai editocinmu sun duba, sun yi ƴan gyare-gyare kafin su saki labarin. Kuma mu kan kira marubuci mu yi magana da shi don gyara gaba.
Game da rubutun batsa kuma shi ma muna duba labarin da aka ɗora ne dama domin duba ƙa’idodojin rubutu da jigo da makamantansu.

Da zarar mun ga rubutu akwai batsa a ciki to, ba mu wallafa shi domin wannan nauyi ne da ya rataya a kawunanmu. Muna iya qoƙarinmu na ganin ba mu taimaka wajen yaixa ɓarna cikin al’aumma ba. Kuma ina son amfani da wannan dama in yi magana kaitsaye da marubuta da ke irin wannan rubutu da su ji tsoron Allah, wannan al’umma tamu ce – ƴaƴanmu ne ciki, da ƙannenmu da iyayenmu – to, mene ne fa’idar taimakawa wajen lalacewarta? Kuma muna da tsari na shirye-shirye daban-daban wajen shawo kan waɗannan matsaloli nan gaba ba da jimawa ba a ɓangarenmu.

Kawo yanzu marubuta nawa ne suke da rijista da ku, kuma guda nawa ne suka ɗora littattafansu?

A gaskiya muna da marubuta masu yawa a Bakandamiya Hikaya. Yanzu haka littattafan da muke da su sun tasamma guda 100 wanda marubuta daban daban suka dora, wasu na kyauta wasu kuma na kuɗi.

Wacce hanya ku ke bi wajen jan hankalin marubuta da ƙungiyoyinsu, don su zo su haɗa gwiwa da ku?

Akwai hanyoyi da dama da muke bi domin ganin marubuta da ƙungiyoyinsu sun zo mun haɗa kai. Misali daga cikin su akwai Gasar Muhawara da muka shirya wa ƙungiyoyin marubuta kuma aka yi taro domin karrama zakarun wannan gasar da sauran waɗanda suka taimaka wajen cigaban adabi. Muna da niyya kuma za mu cigaba da wannan muhawarar da yardar Allah.

Sannan wata hanya kuma ita ce ta ƙoƙarin sayen rubutu daga wajen marubuta daga vangarori daba-daban – ba wai sai wurin sanannun marubuta ba, muna sayen littafin kowa idan ya cika ƙa’ida. Hakan a ganinmu hanya ce ta tafiya da kowa kuma Alhamdulillah muna ganin sakamako mai kyau.

Ta yaya za ku taimakawa marubuta wajen tsare musu haƙƙinsu na mallaka, ba tare da wasu sun yi musu satar fasaha ba?

Matsalar satar fasaha matsala ce da duk duniya ake fama da ita. Mu a namu ɓangaren mun yi ƙoƙari mun samar da wata fasaha ta kariya, ta yadda duk lokacin da muka wallafa wani rubutu babu wanda zai iya kwafa daga manhajarmu. To, amma idan mun tsare a wurinmu ba mu da hurumin tsarewa idan marubuci ya je kuma ya dora aikinsa a WhatsApp ko kuma wata kafa ta daban.

Wanne buri kamfanin ku ke da shi nan da wasu shekaru masu zuwa?

Burinmu shi ne cikin shekaru kaɗan masu zuwa Bakandamiya Hikaya ta zamo wuri da za a samu duk wani littafi mai nagarta da ake nema. Kuma muna fatan rubutun marubutanmu ya inganta, inda za su iya gogayya da sauran takwarorinsu na kudu da ma duniya baki ɗaya – ingantaccen rubutu shi ke kai marubuci ko’ina a duniya.

Shin ke ma marubuciya ce? Waɗanne littattafai ki ka rubuta?

Ni ba marubuciyar labaran ba ce, ina dai rubutu akan fannoni daban-daban, musamman kan fasahar zamani cikin harsunan Turanci da Hausa. Za a iya duba wasu daga cikin rubuce-rubuce na a penprofile.com

Yaya alaƙarki take da sauran marubuta da suke hulɗa da ku?

Muna da alaqa mai kyau da marubuta da dama musamman waɗanda suke ɗora littattafansu a Bakandamiya Hikaya. Akwai marubuta da dama da na ke girmamawa kuma ina jinjina wa baiwar da Allah Ya yi musu a wannan fannin.

Su wanene jagororin wannan kamfani, kuma wacce ƙwarewa suke da ita da za su tabbatar da ingancin tsarin manhajar Hikaya?

Jagora na farko a Bakandamiya shi ne jagoran da ya kafa wannan kamfani namu, wato Malam Lawan Ɗalha. Malamin Jami’a ne da ya ɗebe shekaru sama da ashirin yana karantarwa a makarantun gaba da sakandare daga Nijeriya har Ƙasar Saudi Arabia. Ƙwararre ne a gefen kimiyyar harshe, wato linguistics, musamman ilimin harshen Turanci. Yana da rubuce-rubuce da dama a wannan ɓangaren, sannan yana da sha’awa da ƙwarewa a harkar fasahar zamani sosai. Shaidar ƙwarewar shi a fannin fasahar zamani shi ne ya haifar da wannan manhajar da sauransu da na ambata a baya. Za ku iya duba bayanai da wasu ayyukan shi a lawandalha.info

Mutum na biyu kuma ita ce, ni, Rahmatu Lawan Ɗalha. Na yi digirina na farko ne a fannin sarrafa fasahar sadarwa (Management Information Systems) wanda aikinmu shi ne sarrafa yadda kamfanoni da ma’aikatu ke amfani da fasahar sadarwa a ayyukansu, domin a samu inganci da cigaba a ayyukan da suke gudanarwa. ɗaya daga cikin hanyar da na ke bayar da gudunmawa ta wajen cigaban wannan manhajar ita ce wajen jagorantar tafiyar da tsarin manhajar Hikaya da ake saukewa a wayoyin hannu, da sauran ayyukan da muke gudanarwa.

Muna da wasu mutane da dama kuma da suke bayar da gudunmawa saboda ƙwarewa da gogewarsu a vangarori masu yawa domin cigaban wannan kamfani.

Wanne ƙalubale ku ke fuskanta kawo yanzu tunda ku ka fara gudanar da wannan manhaja?

A duk wata tafiya dole sai an samu ƙalubale to, mu ma a Bakandamiya muna fama da irin namu. Wasu daga ciki sune na fama da muke yi da wasu marubutan wajen turo mana rubutu da ba a tace shi ba, muna wahala sosai akan wannan. Wani ƙalubalen kuma shi ne wajen masu hulɗa da mu, duk da cewa mun yi ƙoƙarin sauƙaƙa abubuwan, kuma zuwa yanzu muna ganin sauƙin abin a hankali. Fatanmu nan ba da jimawa ba duk wannan zai zama tarihi.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki ko aikin da ku ke?

Akwai dai wata karin magana da kakata ke faɗa tun muna yara, inda ta kan ce, “Rabu da kowa ka kama Allah!” Ma’ana mutum ya yi iya ƙoƙarinsa a rayuwa wajen hulɗa da mu’amala, banda cutarwa ko wulaƙantarwa to, idan duk ka yi wannan kar abinda mutane za su yi ko cewa ya zame maka matsala. Gaskiya wannan maganar ta yi tasiri sosai gareni.

Na gode.

Ni ma na gode.