Tinubu ya raba wa ministcoinsa ma’aikatu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da ma’aikatun da ministocinsa za su riƙe.

A ranar Laraba Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana jerin sunayen sabbin ministocin da kuma ma’aikatar da kowannensu zai jagoranta:

Ga jerin sunayen ministcoin da ma’aikatunsu:

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani – Bosun Tijani

Ƙaramin Ministan Muhalli – Ishak Salaco

Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki – Wale Edun

Ministar Harkokin Teku da Tattalin Arziki – Bunmi Tunji

Ministan Lantarki – Adedayo Adelabu

Ƙaramin Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma – Tunji Alausa

Ministan Ma’adinai – Dele Alake

Ministan Yawon Buɗe-Ido – Lola Ade-John

Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola

Ministan Kasuwanci da Zuba Jari – Doris Anite

Ministan Wasanni – John Enoh

Ministan Abuja – Nyesom Wike

Ministar Al’adu – Hannatu Musawa

Ministan Tsaro – Muhammad Badaru

Ƙaramin Ministan Tsaro – Bello Matawalle

Ƙaramin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sununu

Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Ahmed M. Dangiwa

Ƙaramin Ministan Gidaje da Bunƙasa Birane – Abdullah T. Gwarzo

Ministan Kasafi da Tsare-Tsare – Atiku Bagudu

Ministan Muhalli (Kaduna)

Ƙaramar Ministar Abuja – Mairiga Mahmud

Ministan Albarkatun Ruwa – Bello M. Goronyo

Ministan Noma da Samar da Abinci – Abubakar Kyari

Ministan Ilimi – Tahir Maman

Ministan Harkokin Cikin Gida – Sa’Idu A. Alkali

Ministan Harkokin Waje – Yusuf M. Tuggar

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a – Ali Pate

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda – Ibrahim Geidam

Ƙaramin Ministan Ƙarafa – U. Maigari Ahmadu

Ministan Ƙarafa – Shuaibu A. Audu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai – Muhammed Idris Malagi

Ministan Shari’a – Lateef Fagbemi

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyuka – Simon B. Lalong

Ƙaramar Ministar Harkokin Cikin Gida – Imaan Sulaiman-Ibrahim

Ministan Ayyuka na Musamman – Zephaniah Jisalo

Ministan Albarkatun Ruwa – Joseph Utsev

Ƙaramin Ministan Noma da Samar da Abinci – Aliyu Sabi Abdullahi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *