Zai yi wuya a tarihin ‘yan shekarun da su ka wuce a samu wani tsohon shugaban Amurka da ya sha gwagwarmayar da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald ya sha. Ya tsallake tarko da kadarko iri-iri kama daga na dakatar da shafin sa a kafar labarun yanar gizo na ɗ zuwa fuskantar tuhuma a kotu. Karshe dai za a rantsar da Trump a ranar 20 ga watan nan na Janairu don fara mulki a wa’adi na biyu kuma na ƙarshe da ya samu bayan faɗuwa zaɓe da ya yi a shekara ta 2020. Yanda jam’iyyar Dimokrats ta ture Trump a zaben baya da mamaye majalisar dokoki CAPITOL BUILDING da magoya bayan Trump su ka yi ya kawo dushewar fata kan ɗorewar siyasar wannan taliki. Alwashin sa na neman sake dawowa bayan faɗuwa zaɓe ya tabbata.
Gaskiyar magana ma ba wani sauya salon kamfen ya yi ba daga irin bayanan sa na baya na sanya Amurka a farko da kuma yadda ya ke amfani da kalmomin wankin babban bargo ga abokan hamaiyar sa na siyasa. Wasu ma na ganin ko da ba ma Kamala Harris mataimakin shugaba Biden ce ta tsaya takara da Trump ba zai yi wuya a iya nasara a kan sa don yadda kalaman sa ke burge Amurkawa da dama. Tarihi ya sake maimaita kan sa don kamar yaddaTrump ya kada ta mace Hillary Clinton a zaben baya sai ga shi ya sake karawa da wata matar wacce ma ke cikin fadar ta White House. Hatta jami’in da ya jagoranci shigar da karar Trump ta aikata laifuka bayan faɗuwa zaɓe a 2020 ya yi murabus don dalilan shari’ar ba za ta yi nasara ba tun da Trump ya tsallake har ya dawo kan madafun iko. Hakan na nuna maganar ta sha ruwa ta fuskar gurfana gaban alƙali don mai shigar da karar ya bukaci a janye dukkan cajin da a ka shigar.
Ba shakka Trump na cikin farin ciki kuma tuni har ya kusan haɗa duk jami’an da zai yi aiki da su waɗanda kuma ba a yi mamaki ba don irin hakan ne ma ya yi a baya kuma sauke wani mai mukami ba wani kayan gabar ba ne a wajen Trump. Lokacin da ya yi mulki a baya ya taba canja sakataren harkokin waje alhali tsohon sakataren ya na ziyarar aiki a ƙetare. Haƙiƙa akwai masu nuna fargaba kan Trump ka iya dawo da manufar sa ta rage ba da dama ga ma’aikata ko baki daga ƙetare su samu guraben ayyuka a Amurka ko kuma rashin sabuntawa wasu VISA da hakan kan tilasta su ficewa daga kasar. Koma dai yaya a na sa ran samun sauyin manufofi zuwa sassauci don dacewa da yanda duniya ta ke ciki yanzu wajen gwagwarmayar tasiri a duniya tsakanin manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ko karfin soja.
Kuma ko yaya yanayin hare-hare da a ka kai na neman hallaka Trump a kamfen su ke da sahihancin bayanai, ba za a yi mamaki ba in Trump zai rage zama shugaba mai sarƙaƙiya. Tsallake rijiya da baya da ya yi ka iya sanya shi rage taurin zuciya hakanan darashin mutuwar tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter a shekaru 100 a duniya. Wannan zai iya zama abun dubawa cewa duk dadewar shugaba ko tsohon shugaban Amurka to mutuwa ce ƙarshen dukkan talikai.
Masana kiminyyar siyasa da ‘yan diflomasiyya a Nijeriya na sharhi kan dawowar shugaba Donald Trump kan karagar mulki bayan barin madafu a 2020.
Wannan ya zama mai muhimmanci don doguwar huldar diflomasiyya da ke tsakanin Nijeriya da Amurka.
Haƙiƙa yakan zama mizanin la’akari ga manyan ‘yan siyasar Nijeriya ya zama za su iya shiga Amurka da ke nuna ba su da wani kashin kaji da zai hana su rawar gaban hantsi a takarar madafun gwamnatin tsakiya.
In za a tuna a 2019 sai da dan takarar PDP Atiku Abubakar ya ziyarci Amurka don rufe bakin masu caccakar sa cewa indai ya na da gaskiya ya ziyarci Amurka a gani.
Hatta shugaban da ke gado Bola Ahmed Tinubu ya sha da kyar wajen binciken sahihancin kammala karatun sa a jami’a a Amurka da hakan ya kai ga hukuncin kotun koli da ta kawar da tuhumar don ta zo ne bayan zaɓe.
A ranar 30 ga Oktobar da ta gabata shugaban Amurka mai barin Joe Biden ya bugawa shugaba Tinubu waya inda ya gode ma sa bisa yadda Nijeriya ta yafewa ɗaya daga jagororin kamfanin BINANCE masu hada-hadar kuɗin CRYPTO Tigran Gambaryan Ba’Amurke bisa dalilan jinkai bayan tura shi zaman jiran shari’a a gidan yarin Kuje Abuja.
Shin dasawar Nijeriya da Amurka ce ko kuwa cika yarjejeniyar yaƙi da almundahana ta sa Amurka kwanan nan dawowa da Nijeriya dala miliyan 52.88 da tsohuwar mnistar fetur Diezani Allison Madueke ta wawure ta kawo Amurka “wannan yarjejeniya kamar yadda ministan (shari’a na Nijeriya) ya fada ta alamta gagarumar nasara tsakanin gwamnatocin mu biyu kan yaƙi da cin hanci, ƙarfafa bin doka da oda” Inji Jakadan Amurka a Nijeriya Richard Mills.
Ga dawowar Trump mulki, masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Bayero Dokta Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce ya na ganin akwai raguwar barazanar targaden huldar Nijeriya da Amurka a bangaren diflomasiyya, shige da fice, tsaro da sauransu.
Shi kuma tsohon jakadan Najeriya a Trinidad da Tobago Hassan Jika Ardo ya ce Trump dank eke-da-keke ne don haka sai Nijeriya ta sauya salo don samun wanyewa da shi lafiya.
Haƙiƙa yayin da ƙasar Sin ke ƙara neman kusaci da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki, Rasha ke samun gurbin zama a makwabta, Nijeriya na takatsantsan na duk wani matakin juya alƙibla daga Amurka ko ƙasashen yamma.
TSAGAITA WUTA A YAKIN GAZA
Daidai wannan lokacin da a ke haramar mikawa Trump ragama, sai wakilan Hamas da Isra’ila su ka cimma yarjejeniyar tsagaita yakin Gaza. An cimma wannan yarjejeniyar a birnin Doha na kasar katar bayan tattaunawa ta musamman da shafe wata 15 a na zubar da jinin jama’a. Firaministan Katar Sheikh Muhammad bin Abdulrahman bin Jassim Althani ya ba da sanarwar cimma yarjejeniyar da ba da kwarin guiwar za ta kai ga zaman lafiya na bai daya. Yarjejeniyar na nuna za a janye sojojin Isra’ila daga Gaza inda Hamas za ta saki sauran wadanda ta kama ranar 7 ga Oktobar 2023 lokacin da mayakan ta su ka kutsa cikin sassan da Isra’ila ta mamaye ko a ce ta sa shinge. Yakin zuwa yanzu ya yi sanadiyyar kisa ga fiye da Falasdinawa 46,000 akasari mata da kananan yara. Duk da cimma yarjejeniyar sai da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce akwai sauran magana amma a na sa ran daidaitawa yayin da wakilan bangarorin biyu za su bar Doha su tafi birnin Alkahira na Masar don karawa yarjejeniyar armashi.
Dama gabanin nan Gwamnatin shugaba Biden na gaggawa da lokaci don cimma dakatar da yaƙin Gaza kafin tafiyar gwamnatin wato amfani da damar karshe.
A ranar 20 ga watan nan ne ma za a rantsar da zabebben shugaba Donald Trump wanda ke da hamzarin daukar matakai.
Fadar WHITE HOUSE ta ce Biden ya tattauna da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho da ƙarfafa bukatar dakatar da yakin da samun sako kamammun Isra’ila da ke hannun Hamas.
An ruwaito Netanyahu na shaidawa Biden nasarorin da a ke cimmawa a tattaunawa da manyan jami’an sa da ‘yan Hamas a birnin Doha da shiga tsakanin kasar Katar da Masar.
Mai ba wa Biden shawara kan tsaro Jake Sulliɓan ya ce a na gab da cimma yarjejeniya kuma Biden na samun bayanan tattaunawar a kullum.
A baya dai Amurka ta yi ta hawa kujerar na ki a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan kudurin dakatar da bude wutar.
Tuni hakan ya zama abun muhawara tsakanin jama’ar Trump da shugaba Biden wajen nuna wanda ya dace a yabawa da zagi ga samun nasarar. Trump dai na nuna zaben sa da a ka yi ne ya kawo nasarar yayin da Biden ke ganin kokarin sa ne da a karshe ya cimma nasara. An tambayi Biden ko ya dace a yabawa Trump ga kulla yarjejeniyar inda Biden ya amsa da cewa “shin wannan zolaya ne?” Biden ya kara da cewa ya cusa mutan Trump a yarjejeniyar ce don ya zama Amurka na magana da murya daya. Koma dai waye ke da ladar samun sararawar, a gefen Falasdinawa a Gaza sun fantsama kan tituna su na murna wasu na danna hon na mota su na annashuwar za su huta da ruwan boma-boman Isra’ila.
Kammalawa;
Za a jira a ga kamun kudayin Trump a wannan karo musamman ta ɓangaren yaƙe-yaƙe a sassan duniya da ke laƙume rayuka da gurgunta tattalin arziki. Tump dai a baya bai shiga yaƙi kai tsaye ba sai dai daukar wasu matakai kamar harin nan a birnin Bagadaza da ya yi sanadiyyar mutuwar babban kwamandan ƙasar Isra ƙassim Soleimani da kuma kawar da ido lokacin da a ka hallaka dan jaridar nan Jamal Kashoggi a birnin Istanbul. Za a yi sa ran aƙalla dai sararawar zubar da jini a gabar ta tsakiya da yiwuwar sauyin lamuran a yaƙin da Rasha ke yi na kunce ɗamarar Yukrain.