Messi na take-taken komawa Barcelona – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu na ganin cewa Lionel Messi zai tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar PSG, amma kuma wasu rahotanni na nuna cewa ɗan wasan na Argentina na shirin komawa tsohuwar ƙungiyarsa ta Barcelona.

A cewar wani marubucin labarin wasanni na ƙasar Spain Gerard Romero, akwai shakku game da batun tsawaita zaman Messi a PSG.

Ya ce, nasarar da ɗan wasan ya samu ta lashe kofin duniya, ta sauya masa tunani musamman yadda yanzu ya daina fifita lamuran wasa akan wasu abubuwa.

A ’yan makwannin da suka gabata ne dai aka fara saran ɗan wasan mai shekaru 35 zai cimma yarjejeniya da shugaban ƙungiyar Nasser Al-Khelaifi, duk da cewar a ranar 30 ga watan Yuni ne kwantiragin sa da PSG zai ƙare.

Toh sai dai ana ganin babbar hanyar da za ta bada damar Messi ya yi kome Barcelona ita ce rage kaso mai gwabi daga cikin albashin sa ganin halin da ƙungiyar ke ciki na rashin kuɗi.

A shekarar 2021 ne dai Messi ya bar Barcelona inda ya koma PSG suka sake haɗewa da tsohon abokin wasan sa Neymar.