Ministar Jinƙai, Sadiya Farouq, ta jaddada ƙudirinta na yin aiki da ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatar

Daga WAKILINMU

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta jaddada ƙudirinta na kyautata hulɗar aiki da ƙungiyar haɗin gwiwa domin aiwatar da aikin ma’aikatar yadda ya kamata.

Ministar ta bayyana hakan ne a yayin wani biki da ma’aikatar ta shirya mai taken: ‘Makon Farko na Ƙungiya’ a ranar 22 ga watan Disamba, 2022, a ɗakin taro na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya dake Abuja. 

Ministar wadda ta samu wakilcin babban sakatare, Dr Nasir Sani Gwarzo, ta yaba wa ƙungiyar bisa aiki tuƙuru da kuma mutunta jami’an gudanarwa.

Ta bayyana cewa, horarwa haƙƙi ne ga dukkan ma’aikata, kuma sakamakon da yake haifarwa ga yawan ma’aikata ba za a iya wuce gona da iri ba.

Hajiya Sadiya, ta yi alƙawarin bada ƙarin horo ga ma’aikata don ganin sun samu ƙwarewar da yakamata, daidai da kasafin da suke da shi tare kuma da samar da kayan aikin da suka dace, kamar motocin jigilar ma’aikata, sannan ta tabbatar da amincewa kan ma’aikatan da aka yi wa ƙarin girma.

Baya ga haka, minista Sadiya ta sanar da lokacin da ake sa ran ma’aikatar zata naɗe kayanta don komawa sabon muhalinta na dindindim, duk da cewa ba a sanar da rana ba, sai dai ta tabbatar masu da cewa, a farkon shekarar nan da muke ciki. Sannan za a samar da katin tantance ma’aikata mai amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa ga kowanne ma’aikaci.

Daga ƙarshe ta yi kira ga ƙungiyar da ta ƙara zage damtse wurin ƙarfafa kyakyawar hulɗa tsakanin su da masu gudanarwa ma’aikatar.
A nasa jawabin, darakta mai kula da ma’aikta, Mista Tokumbo Rufai, ya miƙa godiya ga masu gudanarwa na ma’aikatar a madadin dukkan ma’aikata, musamman ga ministan da kuma babban sakatare kan damar da suka samu na shirya wannan taro na ‘Makon Farko na Ƙungiya’ irinsa na farko a ma’aikatar.

Ya kuma qara da miƙa godiya ga ilarihin shuwagabanni na ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikata kan yadda suke tafiyar da mu’amalarsu da masu gudanarwa.

A nashi jawabin, shugaban Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan gwamnati Mista Amana Ogwu, ya ce, wannan ne karo na farko da aka tava gudanar da taron na Makon Farko na Ƙungiya tun kafa wannan ma’aikata. Ya kuma miqa godiya ga minista da kuma babban sakatare kan irin goyon bayan da suka bada wurin samar da jin daɗi da walwala ga ma’aikata.

Amana ya ƙara da tunatar da masu gudanarwa nauyin da ke kan ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikata na kutsawa tare tsayawa tsayin daka don ganin sun tabbatar da jin daɗi da walwala ga ma’aikata.

Daga ƙarshe, an gabatar da lambar yabo ga minista da kuma babban sakatare, wasu daga cikin daraktoci tare kuma da ma’aita da suka aikata abin a yaba, kan irin namijin ƙoƙarin da suka yi wurin samar da cigaba a ma’aikatar.