Assalamu Alaikum. Da fatan an yi Sallah Lafiya. Allah Ya maimaita mana, Ilahee Ajeeb.
Su irin waɗannan kalamai na cusa ƙiyayya suna da nau’o’i daban-daban, wasu ta fuskacin siyasa, wasu ta addini, wasu kuma ta zamantakewar yau da kullum. Domin wasu lokuta ko a hira a tsakanin jama’a ma sai ka ga wasu suna furta kalaman da za su ɓata wa ɗan uwansu rai, musamman matasa.
Amma an fi samun irin waɗannan munanan kalamai ta ɓangarorin siyasa da addini.
Wasu na ganin irin waɗannan kalamai da suke furtawa, kalamai ne da kawai suna yin su don su huce hushinsu game da wani abu da ya ɓata masu rai. Kamar yadda wasu kuma, musamman a ɓangaren addini suke yi don su nuna duk wata fahimta da ba tasu ba, to ba ta bisa kan hanya, don haka za su yi ta furta kalaman da dole sai sun tunzura wanda abin ya shafa.
Wannanan ne ya sa muke maganar cewa irin waɗannan kalamai ba su dace ba, domin a cikin addinin ma an yi maganar cewa babu tilasta wa wani ya bi abin da kake yi. Don haka duk irin waɗannan kalamai ba su dace ba, kuma wajibi ne duk wani mai yinsu ya kiyaye, sannan kuma ita Hukuma, wajibinta ne ta ga cewa al’ummarta sun zauna lafiya ta hanyar yi ma tukka hanci.
Ita dai gwamnatin tarayya, ta hannun
Mataimakin shugaban ƙasar, wanda kuma ƙwararren Lauya ne, ta yi wannan tunanin ɗaukar matakin ne bisa la’akari da cewa irin waɗannan kalamai na iya jefa ƙasar cikin wani mummunan hali na yaƙin cikin gida da zubar da jini ba bisa ƙa’ida ba, tare da cusa gabar da ba a san inda za ta ƙare ba.
Sai dai kamar yadda muka faɗa a kwanakin baya, duk wani ƙoƙari da gwamnati ke yi don ganin ta saita al’ummarta ta yadda kowa zai ji daɗin zama, wasu sai sun kalli abin ta wata fuska daban. Inda wasu za su ga ai su an takura masu ne an hana su furta kalamansu da tsarin mulki ya ba su dama da ’yancin yi. Kamar dai yadda wasu suka dirar wa wannan mataki da gwamnatin tarayyar ta ɗauka, musamman a shoshiyal midiya.
Wasu na ganin cewa me ya yi zafi har da gwamnatin za ta sanya wannan fanni na furta kalaman cusa ƙiyayya a cikin aikin ta’addanci. Suka ce, kawai dai gwamnati na ƙoƙarin rufe bakin abokan hamayyarta ne kawai na siyasa, wanda kuma suka ce wannan ya saɓa wa tsarin mulki.
Amma duk da wannan, wasu kuma na ganin cewa ai ba za a taɓa sanya kalaman cusa ƙiyayya a cikin ’yancin faɗin albakacin baki ba, don haka masu furta waɗannan kalamai ba tauye masu damar faɗin albarkacin baki ba ne, nema wa ƙasa zaman lafiya ne.
Saboda haka ni dai a nan ina ganin duk wani mataki da gwamnati ta ɗauka don magance wannan abu da ya zama annoba, to kamata ya yi yaba mata, domin ita dama sanda tun tana ɗanya ake tanƙwarata, in ta bushe, to karyewa za ta yi. Idan aka bar waɗannan abubuwa suna tafiya a haka, to wani bala’Ii ne ke tunkarar ƙasar.
Duk wani mai bibiyar al’ummaran da ke kaiwa da komowa a tsakanin jama’a, ya san cewa irin waɗannan kalamai ba su da wani amfani illa haddasa fitina da rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma, musamman ta ɓangarorin nan guda biyu, addini da siyasa, domin waɗannan fannoni biyu ne abin ya fi muni, ta nan ne mutane ke fakewa da sunan faɗin albarkacin baki, ko faɗin abin da Allah ya ce, alhali suna faɗin son zuciyarsu ne akwai.
Shi wannan abu na kalaman cusa ƙiyayye da wasu suka mayar da shi hanyar cin abinci, ba wani abu ne yake jawowa ba, illa cin mutunci, tozartawa, cin zarafi, tunzura mutum ko tunzura gungun mutane su ɗauki matakin da bai dace ba a kan wani ko wasu, ta hanyar hayaniya da zubar da jini.
Saboda haka kamalaman cusa ƙiyayya manyan makamai ne na samar da hargitsi ko riciki a tsakanin jama’a, wanda kuma yana wuyar gwamnati ta bi duk hanyoyin da za ta bi don ganin haka bai auku ba. Su kuma al’umma, musamman shugabannin addini, wajibinsu su kauce wa irin waɗannan kalamai.
Kusan duk wani rikici da ke faruwa a tsakanin al’umma, na addini ne, siyasa ce, ƙabilanci ko wata fahimta, to duk ya samo asali ne daga wasu kalamai da ake furtawa, waɗanda wasu lokuta ma daga nan inda ake furta waɗannan kalaman ne ake wucewa wajen tashin hankali, a auka wa wanda bai ji ba, bai gani ba. Wanda kuma a wasu lokuta jami’an tsaro kan bi diddigi su kamo waɗanda ake zarginsu da furta irin waɗannan kalaman.
Rashin ɗaukar matakin gaggawa kan irin waɗannan abubuwa, to zai iya ƙasa ga wani irin yanayin da ba a san inda zai ƙare ba. Domin babu wani abu da ke sa ƙasa da al’ummarta su koma baya kamar yaƙi, kuma shi wannan abu na kalaman cusa ƙiyaye, ba abin da yake haddasawa kamar yaƙi a tsakanin al’umma.
Don haka ashe ya zama wajibi ga gwamnati ta ɗauki irin matakin da ta ɗauka na nuna ba sani ba sabo kan duk wani aka samu yana furta irin waɗannan kalamai.
Saboda haka don Nijeriya ta ɗauki matakin hukunta masu irin waɗannan kalamai, ba ita ce farau ba, domin ƙasashe da dama sun riga sun ɗauka tuntuni. Misali, ƙasar Belgium ta yi wannan doka a 1981, Brazil a 1988, Canada a 1990. Haka ma ƙasshen Faransa, Germany, Japan, Afrika ta Kudu, Denmark, Finland da dai sauran ƙasshen da dama, inda ma a ƙasar Canada aka sanya cewa duk wanda aka kama da laifin furta kalaman cusa ƙiyayya, zai kwashe shekara biyar a gida kaso.
Daga Malam Sa’idu. 08068094932.
