Mu kori kamfen ɗin siyasar ƙabilanci a Arewa

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

‘Yan siyasar da zallawa su ka so su zama iyayen gidansu, sun ƙi sauraronsu don haka su ka zama ‘yan barandar maciya bulus. Kowa ya san ba mahaluƙin da ya isa ya yi siyasar ƙabilanci a Arewar Musulmi ko ma a ce kokuwar Arewa kuma duk mai ƙoƙarin haka za ka taras ɗan barandar AIFOB ne. Zallawa ‘yan “GEN Z” ba ma abun da su ka sani sai makirci da a ke lakkana mu su. Kawai dama ba Hausawa ba ne balle su san cewa ba wanda ya isa ya raba Hausawa da musulunci da karyar wai wasu ‘yan ta’adda na ware iya Hausawa su kai mu su hari ko su sace su. Ai ni kai na na kawo mu ku mutanen da a ka sace kuma sun tabbatar da ba abun da ya alaƙanta ‘yan ta’adda da ƙabilanci sai zaluncinsu kawai. Ga labarin Sarkin Fulanin Bungudu, ga na tsohon darakta a gwamnatin tarayya Bappayo Samanja Maudo ga ma Malam Ali Tukur Gantsa da a ka sace tare da tsohon dan majalisar Abba Anas Adamu wanda ta kai ga sanadiyyar rasa ran Abban.

A watannin baya Zallawa na yayata hotunan wasu ‘yan siyasa da su ke tsammanin za su saurare su don amfani da su wajen ruguza Arewa. Shin zuwa yau din nan da na ke rubutu, akwai ko daya daga ‘yan siyasar da ya ce shi BAZALLE ne ko BATSANTSE ne? shin mai ya sa su ka yi majalisi a GIDAN MAMBAYYA amma ba ɗan siyasa da ke gado kai ko ma wani sananne da ya halarci taron? Haba ai duk wanda ya yarda ko hoto ya ɗauka da Zallawa zai ga sakamako a akwatin zaɓe. Har abada Zallawa ba za su ci nasara kan Arewa ba.

Kamuwar da Allah ya yi mu su bayan sun gama cin zarafi da yin sharri ba adadi ga Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, sai caraf tafiyar ta haɗa Kwankwaso da Peter Obi da su ke ɗora hadda hotunansa a shafukansu wai Obi ya fi mu su Sir Ahmadu Bello. Tun daga nan maganar Obi ta mutu murus a farafagandar Zallawa. Shin Sanata Barau Jibrin da su ke maƙalewa wai Bahaushe ne, bai taɓa yin siyasa a doron kabila ba kuma a haka ya ke samun nasara. Ba Bazallen da ya isa ya tinkari ofishin Sanata Barau. Ko dan majalisa Alhassan Ado Doguwa, wannan dama na ja hankalinsa ko hayar gidansa kar ya bar wani Bazalle ya bi balle har ma ya gaisa da maƙiya Arewa.

Shin Gwamna Dauda Lawal ya taɓa zama ko sau ɗaya da wani Bazalle? Yayin da Zallawa ke cin mutuncin Bello Matawalle a lokaci guda su na yabon Dauda sai caraf Matawalle da Dauda su ka dawo ƙarƙashin inuwa ɗaya su na dariya da hakan ya turawa Zallawa baƙin ciki marar misali don Zamfara ta Zamfarawa ce ba masu neman tada fitina ba.

Shin aikin wa Zallawa ke yi ta hanyar sukar Sanata Shehu Buba wai Bafulatani ne? Na tabbata jami’ai za su binciki gaskiyar lamuran nan don abun da babu shi ne kaɗai ‘yan siyasa ba za su iya amfani da shi a neman dauwama ko hawa madafun iko ba.

Mu a Arewa musulmi ya yi addininsa, Kirista ma ya yi addininsa, gargajiya ma ya yi nasa amma shaidu sun nuna yaƙin duk kan masu TAUHIDI ya dosa. KOB da ROB Falanki da Falle duk sun kafa tarkon fito na fito da TAUHIDI don ba su lura da cewa KALIMATULLAH HIYAL ULYA.

Sam ban so yin magana kan lamuran da za su iya shafar sharhin siyasa yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa inda da alamu wasu su ka zama indaroron da ke zubo bayanai ko ba a tantance ba matuƙar zai biya muradin farafagandarsu. Mutumin da Zallawa su ka fi ciwa zarafi tun shekaru biyu da su ka wuce shi ne Sanata Shehu Buba daga Bauchi. Ya taba rike kwamitin Majalisar Dattawa kan tsaro inda su ka rika dora ma sa laifin tabarbarewar tsaro. Cikin ikon Allah a ka sauya shi daga kwamitin a ka mikawa wani. Shin bayan an cire Sanata Buba, tsaron ya samu ko a na gidan jiya?, Shin waye ne ma ya maye gurbin Buba a kwamitin? Ban ga wani Bazalle na maganar ba. 

Ai dama a lokacin su kan zagi Sanata Badaru Abubakar tsohon babban ministan tsaro kuma su ka yi ta shewa lokacin da ya sauka daga mukamin ko a ka sauke shi. Sai kuma karamin ministan tsaro da ke gado Bello Matawalle wanda su ka yi ta ihu cewa lallai sai an cire shi. Ikon Allah da Gwamnan da su ke kauna don cimma makircinsu Dauda Lawal ya sauya sheƙa zuwa APC kuma a ka gan shi ya na murmushi da Matawalle, shikenan zagin ya tsaya cak kamar an yi ruwa an dauke. Shin tsaron ya inganta ne? Ba a ma maganar yadda su ke fadar abun da su ka ga dama kan mai ba wa shugaban kasa shawara kan tsaro NSA Malam Nuhu Ribadu. Saboda tsarin dimokradiyya a ka zuba mu sui do.

Kar na cikaku da wani zance don kawai na shigo na yi magana kan kalubalen da shugaban GIDAUNIYAR ‘yan Zallawa ya yi na a kawo ma sa “takarda daya” duk da ya kamata ya rubuta magana daya da majalisar koli ta shari’a a Najeriya SCSN ta yi kan a dakatar da kashe Musulmi. Shin dama akwai abun da ya hada Zallawa masoya AIFOB da kashe Muslim?.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da majalisar kolin ta shari’a karkashin Dokta Bashir Aliyu Umar ta fitar da ke bukatar a tabbatar da binciken adalci kan wani zargi da wasu ke yi wa Sanata Shehu Buba da a halin yanzu ke takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a inuwar jam’iyyar PRP. Nan dai na ga ashe wasu sun turo shaidu na bayanan inda wanda a ka zaba cewa lallai ya kawo Shiada, mai suna Aliyu Boderi ya ce ya yafe batun biyansa ladar N50,000 ko N60,000 don wani Bazalle ma ya ce ya kara N10,000. Shin ko daga ina mutanen nan ke samun kuɗi da har tayin lada su ke yi?.

Duk mai son gaskiya ya duba tun kafa majalisar koli ta shari’a da marigayi Dokta Datti Ahmad ya yi a 2001, majalisar ke magana kan dukkan muhimman lamuran kasa da kare Musulmi da sauran al’ummar kasa, lamuran tsaro ba tare da fargaba ko ragawa wani don wai an san shi ba matukar ya yi abun da ba daidai ba. Bayan rasuwarsa a 2021, mataimakinsa Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah ya cigaba da wannan aiki har rasuwarsa a bara 2025 inda a ka naɗa mataimakinsa Dokta Bashir Aliyu Umar da shi ma ya dora kan wannan muhimmin aiki. 

Akwai ɗimbin labaru a jaridu, ga faya-fayan bidiyo na tsayin dakar a samar da tsaro da majalisar SCSN a takaice ta gabatar.

Wallahi a iya adalcin da zan yi wa wanda ke ganin majalisar shari’a ba ta magana ko ma ba ta taɓa magana kan tsaro ko wai a dakatar da kashe Musulmi ba; bai san abun da ya ke yi ba ko ɗan kwangila ne na AIFOB da Midibelawa.

Duk bayan wani majalisi ko taro mai ma’ana a kan samu takarda ko jawabin bayan taron don zayyana abubuwan da a ka cimma. Duk hayaniyar da a ka ta yi wai za a yi taron ranar Zallawa da fakewa da Hausa ta zo ta wuce fyuuuuu amma har an wuce mako biyu ba wani Bazalle da ya fito ya karanta takardar bayan taro! Duk da na lura dama ai ba wata takarda da a ka gabatar a taron da za ta iya shiga wani kundi na ilimi.

Ba masanin harshen Hausa ko daya da ya albarkaci taron da ke nuna rashin asali ko amfaninsa daga duniya har lahira. Yo in ba rashin mutunci da raini ba, a nan Arewa wasu wai su ce za su yi taro da sunan harshen Hausa! To su yi wa Hausa me da me da me da tun kafin a haifi kakanninsu ba shi da shi.

Musamman taron MUNBAYYA wanda ko gidan da a ka yi taron Zallawa ba su iya rubuta sunansa daidai ba don dama ‘yan arufta ne kawai na soshiyal midiya, ba abun da mu ka gani fiye da buga gangar PIANO, rawar koroso da shirgawa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa karya wai ya kawo ALKYABBA A shekarar 1457 alhali sai a shekarar 1463 ma ya hau sarauta. Lallai da ma za a fitar da takardar bayan taro, sai an ba wa masarautar Kano da al’ummar Kano haƙuri da janye wannan ikirari mai munin gaske.

Taron da a ka ce za a nuna tufafin Hausawa na gargajiya amma sai a ka ga wasu sanye da hula hana-sallah

Taron da a ke cewa za a yi wakar gargajiya sai kawai a ka ɗauko gangar PIANO ta Bature a ka yi ta bugawa wani matashi da matashiya su na rangaji.

Taron da a ka ce za a nuna gasar dambe ko sana’o’in Hausawa, sai a ka ga wasu na lakkanawa wani yaro kalmomin ƙin jinin Musulunci.

Taron da a ka gayyaci Sheikh Ibrahim Khalil, amma da ya yi jawabin da ya yi hannun riga da zallanci sai masu martani su ka yi ma sa dirar miƙiya da kalamai na rashin mutunci.

KAMMALAWA

Mu na ƙara godewa Allah da al’ummarmu ta Arewa har kullum ta ke fahimtar Gwarawan Zallawan nan ‘yan barandar AIFOB da Midibelawa; makiya Hausawa ne da Musulunci.

A nan zan dakata da tambaya- Shin wa zai faɗi abu ɗaya tak da al’ummar Hausawa da harshen Hausa su ka ci riba daga taron da dama ba su da shi?

By ukarofi

Leave a Reply