Muhyi Magaji Rimingado Zai yi bikin Sallah a gidan gyaran hali

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Alamu sun nuna cewa tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado zai yi bikin karamar Sallah ne a gidan gyaran hali, bayan da ya gaza cika sharuddan beli da kotu ta bayar,

Ko a kafafen sada zumunta dai anyi ta yaɗa rahoton cewa Muhuyi Magaji ya cika sharuudan Beli amma Jami’an kotun suka ƙi bayar da hadin kai domin sallamarsa, zargin da kakakin kutunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ya musanta

“Kotu ta bada shi Beli kuma ta gindaya sharudda wanda a ƙaida shi ne alƙali ya riga ya gama na sa, kuma zai iya tashi yai tafiyarsa gida ma’aikatan kotu rigistara da akawun kotu da sauran mukarransn kotu su za su tsaya su tabbar da cewa an cika wannan sharuɗɗa na kotu, idan lokacin tashin aiki ya yi ba’a cika wannan ƙa’ida ba babu yadda waɗannan ma’aikata za su yi illah su yi abinda doka ta tsara masu su cike masa waranti su bayar su tafi “

Ya zuwa yanzu dai an shiga hutun ƙarshen mako, yayin da Litinin da Tatata ke zama ranakun hutun ƙaramar Sallah da na Ranar ma’aikata, abinda ke alamta cewa zai yi wahala idan Muhuyi bai yi bikin sallarsa a gidan gyaran hali ba. Yan sanda ne dai suka gurfanar da Muhuyi a gaban kotu mai lamba 56 a ƙarƙashin mai Shari’a Aminu Gabari bayan da suka kamo shi a Abuja bayan da suke masa zargin gabatar da takardun lafiya na bogi ga majalisar dokokin Kano, tun a wancan lokacin anyi ta musayar yawu ta bayan fage, sannan har karo biyu ‘yan sanda na yunƙurin kama shi har gida, amma hakan bai yiwuwa ba.

A yayin zaman kotun na jiya dai an gabatar wa da Muhuyi tuhumar da ake yi masa abinda ya musanta nan take daga nan ne lauyan gwamnati ya nemi a dage shari’ar har zuwa ranar 14 ga watan gobe domin su gabatar da hujjoji su.

To amma bayan dawowa hutun awannin biyu ne kotu ta amince da bukatar lauyan Muhuyi na bayar da belinsa a bisa sharuɗɗan zai ajiye kuɗi naira dubu ɗari biyar tare da mutane biyu da za su tsaya masa waɗanda suka haɗa ɗan uwa ko uba a wajensa da kuma babban limamin masallacin Juma’a na Sharaɗa ko Ja’en.

Alƙalin, ya kuma umarci wanda ake ƙara da ya miƙa takardun tafiye-tafiyensa ga kotun.

Haka kuma an hana Muhyi yin magana a kafafen yaɗa labarai ko a kafafen sada zumunta, har zuwa huɗu ga watan Mayu mai kamawa don a cigaba da shari’ar.