Mun gamsu da matakan da Kwamishinan Kasuwanci ya ɗauka kan zaɓen ƙungiyar ‘Yan Katako a Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Kwamared Shehu Aikawa na ƙungiyar kasuwar ‘yan katako da ke Rijiyar Lemo Kano, ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Kano ta ɗauka ƙarƙashin Kwamishinan ma’aikatar ciniki da masana’antu Hon. Kibiya na dakatar da zaɓen da aka yi wa shuwagabannin kasuwar don kawo masalaha da zaman lafiya a tsakanin ‘yan ƙungiyar da jama’ar kasuwar katako ta Rijiyar Lemo abin nuna gamsuwa ne da yarda da abin da gwamnatin take yi, ƙarƙashin jagora Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta yi a wannan lokaci, kamar dai yadda Kwamared Shehu Inuwa Aikawa, wanda aka dakatar da zaɓen da aka yi masa ya bayyana a wannan lokaci.

Haka kuma ya ce, zaɓen da aka gabatar a kasuwar ya nuna shi ne ya samu gagarumar nasara da ƙuri’u masu yawa, amma kasancewar zaɓen ya zo da tirjiya da kuma zargin arangizon ƙuri’u da kuma ɗaya ɓangaren da suka shiga zaɓe ya yi haka ce ta kawo tirjiya, wanda har ya sa gwamnati ta kirawo su, aka tattauna aka yi masalaha ba don bai yi nasara ba, domin dai masalaha da zaman lafiya da gwamnati ke buƙata a kasuwar da ma Jihar Kano baki ɗaya, amma ya ce duk lokacin da aka zo zaɓe, da ikon Allah nasara na tare da mai haƙuri a kowane al’amari na rayuwa. Kamar yadda wannan zaɓe aka gabatar da shi ƙarƙashin masu haƙƙin gabatar da zaɓe da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a lokacin da ya gabata.  

A nasa ɓangaren kantoman riƙo na ƙungiyar kasuwar ‘yan katako Rijiyar Lemo Kano, Alhaji Yusuf Tanko Abdullahi, ya ce a matsayinsa na wanda aka naɗa a matsayin kantoma na riƙon shugaban ƙungiyar na Jihar Kano, babban burinsu shi ne zaman lafiya a wannan kasuwa da ƙungiyar da ma Kano baki ɗaya, kuma za su yi aiki tuƙuru wajen ganin an zauna lafiya kuma an yi zaɓe lafiya gwargwadon lokacin da kuma ta ɗiba kuma ta ga ya dace a yi wannan zaɓe na ƙungiyar ‘yan katakon Rijiyar Lemo, reshen Rijiyar Lemo Kano.

A ƙarshe ya yaba wa ‘yan kasuwa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a kan harkar wannan kasuwar katako ta Rijiyar Lemo inda kuma ya ƙara da cewa ganin a na cikin yanayin hunturu a wannan lokaci Alhaji Yusuf Tanko Abdullahi, na jagorantar kwamiti na musamman domin wayar da kan ‘yan kasuwa wajen kaucewa tashin gobara, kasancewar katako makamashi ne kuma abun wuta ne, mai kama da fetur, Allah ya kare mu.

By ukarofi