Murza gashin baki da Buhari ya yi

A yamma ranar 1 ga Yuni, 2021, Shugaban Ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya yi wani furuci ma jan hankalin da ya dace da buƙatar Nijeriya da ’yan Nijeriya, wanda kuma ba kasafai ake samun sa aikata irin waɗannan kalamai ba. A taƙaice ma dai, gwamnatinsa ba ta cika yin irinsu ko da da yawunsa ne tun bayan kafuwarta a watan Mayu na shekara ta 2015 zuwa yanzu a watan Yuni na shekara ta 2021.

Da yawa suna alaƙanta hakan da kasancewar Shugaban Ƙasar dattijo, Hausa-Fulani, ɗan Arewa, gogagge da sauran ɗabi’u makamantan hakan, waɗanda su ne suke sanya ake kallon gwamnatin a matsayin mai yakana da alkunya da yawa. Don haka sai ka ga wasu abubuwa suna ta faruwa, amma gwamnati na bi a hankali wajen shawo kan lamarin. Sai dai kuma daga dukkan alamu, waɗancan kalamai na Shugaba Buhari na nuni da cewa, ta yiwu zai ɗauki sabon salon tunkarar matsaloli.

Ba wasu kalamai Shugaban ƙasar ya yi ba, face barazana da kuma mayar da martani ga masu tayar da hankula da su ke kai hare-hare ga ofisoshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, wato INEC, musamman a yankin Kudu maso Gabas, inda suke ƙona ofisoshin tare da aikata kisan gilla a guraren. Wani ɓangare na kalaman na Shugaba Buhari ya yi zafin da hatta manhajar Tiwitasai da ta cire shi, saboda a ganinta, lafazin da ya yi amfani da shi, ya sa~a da dokoki da ƙa’idojin aikawa da saƙaonni a manhajar. Abin tambaya a nan shi ne, shin mene ne haƙiƙanin maganar da Shugaban Ƙasar ya yi ne kuma mene ne tasirinta da dacewarta?

Furucin da ya janyo cece-kucen cikin lafazan shugaban shine, inda ya ke cewa, “da yawan waɗanda a yau suke aikata wannan aika-aika ba su da girman shekarun da za su san irin lalatawa da asarar rayukan da suka faru a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya ba. Daga cikinmu, waɗanda suka kasance a fagen daga tsawon watanni 30, za su ɗauki mataki akansu ta hanyar irin yaren da suka fi fahimta.” Wannan shine, furucin da ya janyo hatta Tiwita sai da ta cire saƙon.

To, amma a cikin cikakken furucin da Shugaba Buharin ya furta lokacin da ya ke amsar baƙuncin Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, cewa ya yi, “Ina amsar rahoton tsaro na kullum kan muhimman gine-ginen gwamnati, kuma a bayyane ta ke cewa, masu ɗaukar nauyin aikata hakan suna son ganin bayan wannan gwamnatin ne.

Duk mai son lalata tsarin, ba da jimawa ba rayuwarsa za ta girgiza. Mun ba su lokaci da yawa.
“Yau na amshi bayani daga Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) kan jerin hare-haren da ake kai wa kadarorinta a faɗin ƙasar. Waɗannan hare-hare ba abubuwan amincewa ba ne, kuma ba za mu bar masu ɗaukar nauyinsu ba su cimma mummunar aniyarsu.

“Na bai wa Hukumar INEC tabbacin cewa, za mu ba su dukkan abin da suke buƙata, don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata, don kada ma wani ya ce, ba mu son barin mulki ko kuma mu na son zarcewa zango na uku. Babu wani uzuri abin karba ga kasawa. Za mu biya wa INEC dukkan bu}atunta.

“A ɓangaren tsaro, mun canja Shugabannin Tsaro da Babban Sufeton ’Yan Sanda na ƙasa, kuma mun umarce su da su tabbatar sun tashi-tsaye wajen ganin sun fuskanci ƙalubalen da ke gabanmu. Ba sauran uzuri kan waɗanda suke faman ganin sun ɗaiɗaita ƙasarmu ta hanyar haɓaka ayyukan laifi da ta’addanci.”

Daga nan ne, Shugaba Buhari ya rufe kalamansa da waccan barazana, wacce ba kasafai ya ke yin irinta ba, inda ya yi hannunka mai sanda da cewa, masu aikata ta’addanci a kadarorin hukumomi su ma za su fuskanci irin abin da suke aikatawa daga ɓangaren gwamnati.

Daga nan ne fa sai masu goyon bayan aikata irin wancan ta’annati da kuma waɗanda suka jahilci irin barazanar da hakan ke yi ga zaman lafiyar kowa suka duƙufa wajen suka da yin allawadai kan kalaman na Shugaban Ƙasa. To, a haƙiƙanin gaskiya, idan aka yi la’akari da halin da ƙasar ke ciki a halin yanzu na matsalolin tsaro da kuma tunkarar shirye-shiryen Babban Zaɓen Ƙasa na 2021, sai dai ma a ce, lafazan na Shugaba Buhari sun makara, amma ba a dai a ce ba daidai ba ne, domin irin waɗancan ƙungiyoyi na ɓangaranci da Kudu Maso Gabas, kamar IPOB, wacce ke ɗaukar nauyin irin wannan ta’addanci da ake yi wa kadarorin ƙasa da kuma al’ummar yanki Arewa da ke zaune a yankin ko kuma suka kai ziyara, kamar yadda aka kashe tsohon Mai Bai Wa Shugaban Shawara kan Harkokin Siyasa, Barista Ahmad Gulak, a yankin nasu, akwai bu}atar duk wani shugaba nagari mai kishin ƙasa da al’ummarsa ya yi amfani da ƙarfin ikon da Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ya ba shi, ya taka musu burki.

Su na kashe rayuwa, su na ɓarnata dukiyoyin al’umma, su na hana wa mutane zaman lafiya da kwanciyar hankali, su na haramta wa wasu ba’arin jama’a zama a yankinsu, saɓanin yadda Kundin Tsarin Mulki ya halasta musu, to mene ne laifi don shugaba ya fito ya ce, zai dakatar da irin wannan ta’annati ko da kuwa ta hanyar aikata musu makamancin abin da suke aikata wa sauran ’yan ƙasa ne?

Mu a nan Manhaja, muna goyon bayan Gwamnatin Tarayya da Fadar Shugaban Ƙasa da ma duk wata hukuma da ke da ruwa da tsaki wajen ganin an tabbatar da an magance matsalar tsaro tare da da}ile duk wata ƙungiya ko mambobinta da ke kawo cikas ga yiwuwar haka, domin rai bai fi rai ba! Wanzuwar samun zaman lafiya, yalwa, kwanciyar hankali, lumana da wadata suke gaba da komai da kuma kowa!