Mutane 13 sun nutse a kogi, 22 sun ɓace yayin da suke tserewa daga farmakin ‘yan bindiga a Zamfara

Spread the love

Aƙalla mutane 13 ne suka mutu inda wasu 22 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a ƙaramar hukumar Gummi dake Zamfara ranar Juma’a da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewar, Kwale-kwalen na ɗauke ne da mazauna ƙauyen Birnin Magaji a ƙaramar hukumar ta Gummi yayin da suke tserewa daga wani harin ‘yan bindiga da suka kai wa al’ummar garin da sanyin safiyar Juma’a.

Malam Basiru Ibrahim da ke ƙauyen a wata hira da wakilin mu ta wayar tarho, ya bayyana cewar waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibinsu mata ne da ƙananan yara daga Danmaga, Tungar Maigunya, da kuma Nasarawar Kifi, a lokacin da suka garzaya zuwa kogin domin neman tsira.

Wani ma’aikacin lafiya a Birnin Magaji, Shehu Mohammed, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, babban ɗansa da wasu ’ya’yan sa biyu na daga cikin mutane 13 da suka mutu a lokacin da jirgin ya cika makil da mutane.

Maidamma Dankilo, hakimin Birnin Magaji, ya tabbatar da mutuwar mutane 13 daga cikin kwale-kwalen, an ceto 22, wasu 22 kuma ba a gansu ba sun bi ruwa har yanzu.

Wani ganau, Malam Bashiru, ya koka kan yadda al’umma ke ci gaba da rasa rayuka a duk shekara sakamakon irin wadannan haɗurran saboda rashin isassun kayayyakin sufuri.

Ya yi kira ga gwamnati da hukumar NEMA da su samar da tallafin jin ƙai da ƙarin jiragen ruwa ga mazauna ƙauyukan da gonakinsu da sana’o’insu suka dogara da sufuri ta ruwa.

Hakimin ƙauyen Nasarawar Kifi, Alhaji Muhammadu Chigari, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana yanayin da al’ummar yankin ke ciki a matsayin abin baƙin ciki.

Ya bayyana cewa waɗanda harin ya rutsa da su sun haɗa da matan gida takwas, jarirai uku, da kuma matasa huɗu, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda suka ɓata.

Tuni dai aka yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

A halin da ake ciki, shugaban ofishin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), reshen Sokoto, Aliyu Shehu, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho faruwar lamarin, duk da dai bai iya tantance adadin waɗanda suka mutu ba.

Ya ce tawagar NEMA tare da haɗin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara (ZEMA) za su ziyarci wurin domin tantance adadin waɗanda abin ya shafa da kuma samar da kayan agaji ga iyalansu.

“Mun samu labarin wannan mummunan lamari a yau, hukumar bada agajin gaggawa ta Zamfara da tawagar mu za su kai ziyara can gobe, domin ba za mu iya tabbatar da adadin wadanda abin ya shafa ba tukuna.

By ukarofi