Mutane 13 sun rasu, ana riƙe da yara 12 har yanzu – Ba’asin ‘yan Kwara da suka shaƙi iskar ‘yanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu daga cikin mutanen ƙauyukan Woro da Nuku na Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara da suka shaƙi iskar ‘yanci bayan harin ranar 3 ga Fabrairu, sun bayyana cewa mutane 13 sun rasu a lokacin da suke hannun ‘yan bindiga, yayin da kuma har yanzu akwai yara guda 12 da ke komar ‘yan ta’adda.

Sun bayyana haka ne ga manema labarai bayan Gwamnatin Jihar Kwara ta karɓi baƙuncinsu a hukumance, inda suka bayyana yadda suka tsinci kansu a daji da rayuwar cin abinci sau guda a yini na tsawon kusan watanni shida.

Mutanen na daga cikin mata da yara guda 176 da wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka sace su, bayan ƙaddamar da wasu hare-hare a ƙauyukan Woro da Nuku.

A ranar Laraba ne mutanen suka shaƙi iskar ‘yanci, inda wata daga cikinsu mai suna Nafisat Abdulfatai ta ce har yanzu akwai yara da dama acikin dajin, saboda masu garkuwar sun shaida musu cewa matuƙar suka yi yunƙurin tafiya, to za su zama bayi.

Ta bayyana cewa, duk da cewa ‘yan ta’addar ba su cika dukan su ba, amma suna zama cikin halin yunwa mai tsanani da kuma takura acikin jejin.

A cewarta, sun yi ta kwana a buɗaɗɗen waje na tsawon watanni kana daga bisani aka kai su wani rufaffen waje bayan yara da dama sun rasu sakamakon rashin samun wadataccen abinci da kulawar da ta dace da su.

Kazalika, ta ce mata masu juna biyu da dama sun haihu amma kuma jariran sun rasu. Ta ce kimanin mata shida ko bakwai ne hakan ya faru da su, inda wasu kuma suka yi nasarar koma wa gida da nasu a raye.

By Babaji