Mutane da dama sun mutu sakamakon gobarar tankar mai a Neja

Daga USMAN KAROFI

Akwai fargabar mutuwar mutane da dama yayin da wasu suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai a yankin Dikko Junction, ƙaramar hukumar Gurara ta Jihar Neja.

Wani ganau ya bayyana cewa wata mata mai juna biyu da wata mace da jariri mai makonni guda sun rasa rayukansu a gobarar. Shaidu sun ce yawan waɗanda suka mutu ya zarce mutum 30, duk da cewa ba a samu tabbacin haka ba.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Neja tana bakin ƙoƙarin ta domin kashe wutar, amma har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi game da lamarin.