Daga ABUBAKAR M TAHEER
A jiya Talata da misalin sha ɗaya na dare wata tanka ɗauke da man fetur da ta taso daga Kano zuwa Nguru ta faɗi a kusa da Khajida University Majia.
Cikin wata sanarwar gaggawa da jami’an hulɗa da jama’a na hukumar ‘yan sanda ta Jihar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adam ya fitar da safiyar yau, ya bayyana yadda lamarin ya afku.
Bayan faɗuwar tankar ke da wuya man ya rinƙa kwarara magudanan ruwa wanda al’ummar garin su ka fito domin kwasar man fetur ɗin, nan take wuta ta kama inda nan take nutum 94 sun ƙone ƙurmus.
Sauran mutum 50 kuma sun samu munanan raunuka inda aka garzaya dasu babban asibitin Ringim domin amsar magani da kulawa.
Kwamishinan ‘yan Sanda CP AT Abdullahi ya jajantawa al’ummar Majia dama jihar Jigawa baki ɗaya kan wannan iftila da ya same su tare da adduar Allah ya jiƙan wanda su ka rigamu gidan gaskiya.
Ya kuma buƙaci al’umma da su rinƙa kulawa sosai da lamarin faɗuwar tankar mai wanda take saurin kamawa da wuta bayan faɗuwar ta.
Zuwa haɗa wannan rohoton al’ummar garin na Majia na cikin halin kaɗuwa bisa wannan mummunan ifitila’i daya afka musu.
