PDP ta dawo da Damagum da wasu jigogin jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake samu rikici acikin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya (PDP), ƙungiyar gwamnonin jami’yyar ta ƙudiri aniyar haɗe kan mambobinta tare da kawar da duk wata saɓani da ake samu a tsakanin su.

Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Abdulƙadir Bala Muhammad ya bayyana hakan, inda ya ce ya soke dakatarwar da aka yi wa wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyyar.

Gwamna Bala ya faɗi hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar jim-kaɗan bayan kammala wani taron gaggawa da mambobin PDP a Abuja.

Kawo yanzu ana samun raɗeraɗin cewa ba a kai ga warware matsalolin da ke cikin jam’iyyar ba kasancewar akwai mambobin da ke kotu kan waɗansu ƙararraki.

Saidai, sakamakon zaman da aka gudanar ya nuna Umar Damagum zai cigaba da zama shugaban jam’iyyar na ƙasa a matsayin mai riƙon ƙwarya.

Bala Muhammad, ya cigaba da cewa, ya zama wajibi kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya yi ƙoƙarin samar da daidaito akan al’amuran da suke kawo cikas ga harkokin PDP don kai jam’iyyar ga nasara a zaɓukan da aka sa a gaba.

Saboda haka ne ya sanar da soke batun dakatarwar, ya na mai cewa hakan shine hukuncin da ƙungiyar gwamnonin ta yi.

Haka nan, jami’yyar ta yi albishir ga magoya bayanta cewa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta yi nasara a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

By Babaji