Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mutum tara suka mutu wasu 11 suka sami raunuka a wani mummunan haɗari da ya afku a hanyar Malumfashi zuwa Kafur a Jihar Katsina.
Bubban kwamandan kiyaye haɗaruka na ƙasa a Katsina Aliyu Ma’aji ya sanar da haka da yake hira da manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa motar haya ƙirar Hummer mai ɗauke da mutane 20 ya yi haɗari sanadiyyar gudun wuce kima.
Ma’aji ya yi kira ga masu ababen hawa da su guji tuƙin ganganci da gudun wuce kima.
Yace duk da ƙoƙarin gwamnatin Jihar Katsina na inganta da gina hanyoyi na zamani a jihar”tuƙin ganganci sai ƙaruwa yake da haifar da rasa rayuka”inji kwamandan
