Na shafe watanni Ina haɗa jinina da zoɓon sayarwa, inji mai cutar ƙanjamau

Daga WAKILINMU

Wata mata da kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kanta ta bayyana cewa tana amfani da jini mai ɗauke da ƙwayoyin cutar ƙanjamau wajen haɗa zoɓon da ta ke sayar wa jama’a.

Matar wadda ta yi wannan ikirari ta bayyana hakan a yayin wani shiri mai taken ‘hada-hadar kasuwanci’ na MarketRunz da gidan rediyon Wazobia FM ya saba watsawa a duk daren ranar Laraba.

A cikin shirin dai masu sauraro kan kira ta lambar waya su faɗi ababen da suke aikatawa a bayan fage kan harkokinsu na kasuwanci waɗanda abokan hulɗarsu ba su da masaniya a kai, duk da cewa sukan yi hakan ne ba tare da wani alfahari ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, matar ta ce babbar manufar wannan aika-aika da tak e yi ita ce yada wannan cuta mai karya garkuwar jiki a tsakanin al’umma.

A cewar wannan mata, “na je aisiti watanni shida da suka gabata sai aka sanar mani da cewa ina ɗauke da cutar HIV.

“Ba ni da kuɗin da zan yi maganin wannan cuta don haka na yanke shawarar ba zan bari na mutu ni kaɗai ba sai dai a yi mutuwar kasko.

“A bisa wannan shawara da na yanke ce na soma zuba jinin jikina a cikin zoɓon da nake haɗawa ina sayar wa mutane masu tarin yawa.

“Na kan samu sirinji na zuƙo jinin sai na haxa zoɓon da shi. Ni malamar asibiti mai aikin jinya amma bayan na samu tabbacin ina ɗauke da wannan cuta sai na daina zuwa aikin.

“Ba na murna da wannan abu da na ke aikatawa, amma Ina cike da farin cikin cewa ba zan mutu ni kaɗai ba.

“A yanzu watanni shida ke nan ina wannan abu kuma ina addu’a Allah zai yafe min.”